Isra’ila ta gudanar da bikin Tunawa da kisan kiyashin da Hitler yayi wa yahudawa kusan miliyan 6 wanda ake Kira da (Holocaust a turance) a fadin ƙasar, domin girmama miliyoyin Yahudawa da aka kashe a lokacin mulkin Nazi da Hitler ke Jagoranta a Yaƙin Duniya na Biyu.
A yayin bikin, an kunna kararrawar sanarwa na ƙasa baki ɗaya na tsawon mintuna biyu da ƙarfe 10:00 na safe, inda al’umma suka tsaya cak cikin shiru domin tunawa da waɗanda suka mutu.
Babban bikin na ƙasa ya gudana ne a Yad Vashem da ke birnin Kudus, cibiyar tunawa da wadanda aka kashe, inda manyan shugabanni na ƙasar suka halarta, ciki har da shugaban ƙasa da Firaminista, domin ajiye furanni da gudanar da bukukuwan tunawa.
Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Israi'lan ke cigaba da yin ruwan bama-bamai a Lebanon da Gaza bayan Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran a yaƙin da suke yi a tsakaninsu.

0 Comments:
Post a Comment