Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta amince da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba, tare da sauran mambobin Kwamitin Gudanarwan Jam'iyyar na Ƙasa (NWC) ba, har sai an kammala shari’ar rikicin shugabanci da ke gaban kotuna.
INEC ta jaddada cewa matsayinta ya dogara ne kan dokokin da ke jagorantar ayyukanta, inda ta ce dole ne a jira hukuncin kotu kafin ta yanke shawara kan halaccin shugabancin jam’iyyar.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da lura da yadda shari’ar ke gudana, tare da bin duk wani hukunci da kotu ta yanke kan rikicin cikin gida na jam’iyyar ADC.

0 Comments:
Post a Comment