Hukumar DSS Ta Kama Wata Matar Da Ake Zargi Da Safarar Makamai a jihar Kano.

Hukumar DSS Ta Kama Wata Matar Da Ake Zargi Da Safarar Makamai a jihar Kano.

Hukumar Tsaron farin kaya na Kasa (DSS) ta kama wata mata mai shekaru 25 mai suna Nafisa Usman a jihar Kano, bisa zargin safarar makamai.

An bayyana cewa Nafisa Usman ‘yar garin Zango, karamar hukumar Kankara, Jihar Katsina ce. 
An kama ta ne a babban tashar mota tana ɗauke da harsasai 200 sabbi da aka ɓoye cikin buhunan gari da shinkafa.

Rahotanni sun nuna cewa ta saya harsasan ne a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa don kaiwa garin Kankara dake jihar Katsina. 
Matar dai ta amsa wa DSS cewa tana cikin wannan harkar tsawon watanni biyu, inda ta bayyana cewa wani da ta ce mai suna Teso, wanda ake zargin yana da alaƙa da wani soja a Lafia, shi ke tsara safarar makaman.

An ce harsashan da ake safara an za'a Kai su ne ga ‘yan fashi da makami da ke dajin Kankara, ciki har da wasu da aka bayyana da sunayen Mallam Haruna da Buba, da Abu. 
Ta kuma bayyana cewa ta gudanar da mu’amaloli na kimanin ₦5 miliyan kafin kama ta.

Hukumar DSS ta ce matar ta nuna nadama bayan kamatan da aka yi.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: