Gwamnan Borno Ya Ba da Naira Miliyan 150 Ga Iyalan Laftanar Kanar Uku da Aka Kashe

Gwamnan Borno Ya Ba da Naira Miliyan 150 Ga Iyalan Laftanar Kanar Uku da Aka Kashe

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayar da gudummawar naira miliyan 150 ga iyalan manyan sojoji uku masu mukamin Laftanar Kanar da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun rasa rayukansu ne yayin fafatawa da ‘yan ta’addan a wasu yankuna masu fama da rikici a jihar Borno. Gwamnan Zulum ya bayyana cewa tallafin na nufin rage radadin da iyalan mamatan ke ciki da kuma yaba wa sadaukarwar da sojojin suka yi wajen kare ƙasa.

Haka zalika, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa iyalan jami’an tsaro da suka rasu, tare da yabawa jarumtakar sojojin wajen yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas.

News Translation in English Language.

Borno Governor Gives N150 Million to Families of Fallen Lieutenant Colonels.

Borno State Governor, Babagana Umara Zulum, has donated N150 million to the families of three Lieutenant Colonels who were killed by Boko Haram insurgents in the state.

The officers reportedly lost their lives while combating insurgents in troubled areas of Borno. Governor Zulum said the donation is intended to ease the suffering of the bereaved families and to honour the ultimate sacrifice made by the officers in defending the nation.

He also reaffirmed that the state government will continue to support the families of fallen security personnel and praised the courage and commitment of the military in the ongoing fight against terrorism in Northeastern Nigeria.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: