Iran Zata Ci Gaba da Taimakawa Kungiyar Hezbollah domin Yaƙi da Amurka da Isra’ila.

Iran  Zata Ci Gaba da Taimakawa Kungiyar Hezbollah domin Yaƙi da Amurka da Isra’ila.

Shugaban Juyin Juya Halin Musulunci na kasar Iran, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya aike da wata wasika ga Sakataren Janar na kungiyar Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, inda ya tabbatar masa da cewa Iran za ta ci gaba da goyon bayan ƙungiyar gwagwarwayar a kokarinsa na yaƙi da abin da ya kira ƙiyayyar ta da “Amurka da Isra’ila”. 

A cikin saƙon, Khamenei ya ce manufofin Iran dangane da tallafawa ƙungiyoyin gwagwarwaya ya samo asali ne daga hanyar jagorancin marigayi shugaba Ayatollah Seyyed Ali Khamenei da kuma darajar waɗanda suka yi shahada kamar Sayyed Hassan Nasrallah — tsohon shugaban Hezbollah. 

Ya ƙara da cewa duƙufa da tsayin daka wajen fuskantar abokan adawa – wato Amurka da Isra’ila – na daga cikin muhimman halaye da marigayi Khamenei ya bari a tarihi. 

Babban jagoran Iran ya yaba da girmamawa da ƙauna da Hezbollah ke nunawa ga ƙasarsa, inda ya ce hakan yana ƙara tabbatar da haɗin kai tsakanin Iran da masu gwagwarmaya a yanki a wannan mawuyacin lokaci na yaƙi. 

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: