Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce duk da cewa tashin farashin man fetur na ci wa ‘yan Najeriya tuwo a ƙwarya, ya kamata su yi godiya ga Allah idan suka kwatanta kansu da wasu ƙasashen Afirka kamar Kenya da sauran ƙasashe.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya, inda ya ce halin rayuwa na da wahala, amma Najeriya na cikin ƙasashen da har yanzu ke da wasu damammaki da ba a samu a wasu wurare ba.
Ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da haƙuri tare da goyon bayan matakan gwamnati na gyaran tattalin arziki, yana mai cewa ana kokarin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin farashin mai da tsadar rayuwa.
Shugaban ya ce gwamnatinsa na sane da ƙalubalen da jama’a ke fuskanta, amma yana ganin akwai bukatar a duba yanayin sauran ƙasashe domin fahimtar cewa Najeriya ba ta cikin mafi munin hali a nahiyar Afirka.

0 Comments:
Post a Comment