Ƙasar Australia ta kafa tarihi bayan ta naɗa Susan Coyle a matsayin shugabar rundunar sojin ƙasar—karon farko a cikin shekaru sama da 125 da mace za ta jagoranci rundunar.
Wace ce Susan Coyle?
Susan Coyle babbar jami’ar soja ce mai mukamin Lieutenant General, wacce ta shafe shekaru da dama tana hidima a rundunar sojin Australia.
Ta shiga soja tun shekarar 1987
Ta yi aiki a yankuna kamar:
Afghanistan da Gabas ta Tsakiya.
A halin yanzu tana rike da mukamin Chief of Joint Capabilities.
Za ta fara sabon mukaminta a watan Yuli 2026, inda za ta maye gurbin tsohon shugaban rundunar.
Wannan naɗin yana cikin wani babban sauyi da ake yi a tsarin rundunar tsaron ƙasar, domin inganta shugabanci da ƙarfafa rundunar.
Wannan shi ne karon farko da mace za ta jagoranci rundunar sojojin ƙasa a Australia inda ya kawo ƙarshen dogon lokaci na shugabancin maza kaɗai.
Naɗin Susan Coyle ba kawai sauyin shugabanci ba ne, illa wata babbar alama ce ta ci gaba a daidaito da damar mata a fannin soja.

0 Comments:
Post a Comment