A wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a Badariya, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, sun kashe wani ɗan kasuwa mai suna Sufiyanu Garba, sannan suka sace matarsa wadda ke dauke da juna biyu.
Harin ya faru ne yayin da ‘yan bindigar suka mamaye gidansu, lamarin da ya jefa al’ummar unguwar cikin tsoro da firgici.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare yayin da ‘yan bindigar suka mamaye gidansu, suka harbe garba kafin su sace matarsa.
Wannan lamari ya jefa al’ummar unguwar cikin tsoro da fargaba, inda mazauna unguwar suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin su.
Jami’an tsaro daga ‘Yan sanda da sojoji sun isa wurin nan da nan, Inda suka gudanar da bincike don gano sauran ‘yan bindigar da Kuma yiwuwar ceto matar da aka sace. Hukumomi sun bayyana cewa za su ƙara ƙarfafa tsaro a yankunan da suka fi fuskantar hare‑hare don kare rayukan fararen hula da rage aikata laifukan ‘yan bindiga.
Iyalan mamacin suna cikin babban alhini yayin da suka bayyana rashin jin dadin su game da rashin tsaro a yankin. Masu lura da harkokin tsaro sun ce hare-haren irin wannan na ci gaba da yi wa al’umma katsalandan, musamman a arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke kai farmaki kan gidaje da kasuwanni a lokuta daban-daban.
Hukumomi sun yi kira ga al’umma da su ci gaba da bada hadin kai wajen bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo ‘yan bindigar da hana aukuwar irin wannan ta’addanci nan gaba.

0 Comments:
Post a Comment