Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu ta Hamas ta bayyana fatan cewa Mojtaba Khamenei, sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, zai ci gaba da tafiyar da manufofin goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa da kuma tunkarar Israel.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙungiyar, wato Izz ad-Din al-Qassam Brigades, ta fitar, ta ce tana da yakinin cewa Iran za ta ci gaba da kasancewa ginshiƙi wajen tallafa wa ƙungiyoyin gwagwarmaya a yankin, musamman a wannan lokaci da rikici ke ƙara tsananta a Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin Iran da ƙungiyoyin Falasɗinu za su ci gaba da ƙarfafa a ƙarƙashin sabon jagorancin ƙasar, domin tallafa wa gwagwarmayar da ake yi don kare haƙƙin al’ummar Falasɗinu.
Hamas ta bayyana cewa tana ganin sauyin jagoranci a Iran ba zai sauya matsayar ƙasar ba, musamman dangane da batun goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa da kuma ƙin amincewa da manufofin Isra’ila a yankin.
Sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei ya karɓi ragamar jagoranci ne bayan rasuwar mahaifinsa, tsohon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ali Khamenei, wanda ya shafe shekaru da dama yana jagorantar ƙasar tare da nuna goyon baya ga ƙungiyoyin gwagwarmaya a yankin Gabas ta Tsakiya.
News Translation in English Language.
Hamas Welcomes Leadership of Mojtaba Khamenei, Says Iran Will Continue Supporting Palestinians.
The Palestinian resistance movement Hamas has expressed hope that Mojtaba Khamenei, the new Leader of the Islamic Republic of Iran, will continue the country’s longstanding policy of supporting the Palestinian cause and confronting Israel.
In a statement released by the group’s military wing, the Izz ad-Din al-Qassam Brigades, Hamas said it is confident that Iran will remain a key supporter of resistance movements in the region, particularly at a time when tensions in the Middle East continue to escalate.
The statement also emphasized that relations and cooperation between Iran and Palestinian resistance groups are expected to strengthen under the country’s new leadership, with continued backing for efforts aimed at defending the rights of the Palestinian people.
Hamas further noted that the leadership transition in Iran is unlikely to change Tehran’s stance on supporting Palestinian resistance and opposing Israeli policies in the region.
Mojtaba Khamenei assumed leadership following the death of his father, former Iranian Supreme Leader Ali Khamenei, who led the country for decades and was known for his strong support of resistance groups across the Middle East.

0 Comments:
Post a Comment