Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa za ta bayar da ladar da ta kai dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano ko gano inda sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, yake ko kuma bayanai kan wasu manyan jami’an gwamnatin Iran.
Sanarwar ta fito ne a karkashin shirin gwamnatin Amurka mai suna “Rewards for Justice”, wanda ke bayar da lada ga duk wanda ya taimaka da bayanai kan mutanen da Amurka ke zargi da hannu a ayyukan ta’addanci ko kuma jagorantar kungiyoyi masu alaka da shi.
Rahotanni sun ce jerin sunayen ya hada da manyan jami’ai kusan goma da ake zargin suna da alaka da rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), wadda Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci.
Daga cikin wadanda ake nema har da wasu manyan jami’an tsaro da gwamnati kamar Ali Larijani, da kuma wasu ministoci da shugabannin hukumomin tsaro.
Gwamnatin Amurka ta ce duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano wadannan mutane zai iya samun ladan kudin tare da wasu kariya, har ma da damar kaura zuwa Amurka idan hakan ya zama dole domin kare rayuwarsa.
Sai dai gwamnatin Iran ta sha musanta zarge-zargen Amurka, tana mai cewa irin wadannan matakai na da nasaba da matsin lamba na siyasa da Washington ke yi wa Tehran.
News Translation in English Language.
US Offers $10 Million Reward for Information on Iran’s New Supreme Leader Mojtaba Khamenei.
The United States Department of State has announced a reward of up to $10 million for information about Iran’s new supreme leader, Mojtaba Khamenei, as well as several other senior Iranian officials.
According to the State Department, the reward is part of the Rewards for Justice program, which offers financial incentives to individuals who provide credible information about people suspected of involvement in terrorism or activities that threaten U.S. national security.
U.S. officials said the offer also covers information related to a number of high-ranking Iranian figures believed to be linked to the Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), which Washington has designated as a terrorist organization.
The announcement comes amid escalating tensions between the United States and Iran over regional security issues and the ongoing conflict in the Middle East.
Under the program, individuals who provide useful information may receive financial rewards and, in some cases, assistance with relocation or protection if their safety is at risk.
Iranian authorities have repeatedly rejected accusations from the United States, describing such measures as political pressure by Washington against Tehran.

0 Comments:
Post a Comment