Gwamnatin ƙasar China ta sanar da cewa za ta bayar da tallafin kuɗi har dala $200,000 domin taimaka wa iyalan ɗaliban Iran da suka mutu sakamakon mummunan harin da Israi'la da Amurka suka kai kan wata makaranta a yankin Minab.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 175, inda mafi yawansu ƙananan yara ɗalibai ne.
Ƙasar China ta ce za a miƙa wannan tallafi ne ta hannun wata ƙungiyar agaji domin taimaka wa iyalan waɗanda suka rasa ’ya’yansu, tare da nuna alhini da jimami kan harin da aka kai wa fararen hula.
Haka kuma jami’an gwamnatin China sun yi Allah-wadai da kai hare-hare kan makarantu da yara, suna mai cewa irin waɗannan hare-hare suna saba wa dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa, tare da tauye mutuncin ɗan Adam.
News Translation in English Language.
China Pledges $200,000 Aid to Families of Iranian Students Killed in School Attack.
The Chinese government has announced it will provide $200,000 in aid to the families of Iranian students who lost their lives in a devastating school attack.
Reports indicate that the attack claimed the lives of nearly 175 people, most of whom were young students.
Beijing stated that the funds will be delivered through a charitable organization to support the families of the victims, expressing deep condolences over the attack on civilians.
Chinese officials also condemned attacks on schools and children, emphasizing that such acts violate international laws of warfare and undermine human dignity.

0 Comments:
Post a Comment