Rahotanni sun bayyana cewa masu kutse ta yanar gizo da ake zargin suna da alaka da kasar Iran sun kai wani babban hari ta yanar gizo kan kamfanin na’urorin kiwon lafiya na Amurka, Stryker Corporation, lamarin da ake ganin shi ne babban harin farko na irin wannan tun bayan barkewar rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka.
A cewar rahotannin tsaro na yanar gizo, wani rukunin masu kutse da ake kira "Handala hacking group" ne ya dauki alhakin kai harin, inda ya yi ikirarin cewa ya goge bayanai daga sama da na’urori 200,000 tare da satar kusan terabyte 50 na bayanai daga tsarin kamfanin.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya haddasa tangarda ga tsarin sadarwa na cikin gida na kamfanin, inda wasu ma’aikata suka bayyana cewa wayoyinsu na aiki da kwamfutoci sun daina aiki na wani lokaci, lamarin da ya shafi ayyukan kamfanin a sassa daban-daban na duniya.
Sai dai kamfanin Stryker Corporation ya tabbatar da cewa an samu matsalar tsaro a wasu sassan tsarin sadarwarsa, amma ya ce babu tabbacin cewa an yi amfani da ransomware ko kuma wani gagarumin malware da zai iya kawo cikas ga kayayyakin kiwon lafiyar da kamfanin ke samarwa.
Masana harkokin tsaro na yanar gizo sun ce wannan lamari na iya nuna yadda rikicin siyasa da soja tsakanin kasashe ke kara fadada zuwa yakin yanar gizo, inda kungiyoyin masu kutse ke kai hari kan kamfanoni masu zaman kansu domin matsa lamba ta fuskar tattalin arziki da kuma ta tunani.
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken tasirin harin da kuma ko akwai wata alaka kai tsaye da hukumomin gwamnatin Iran.
News Translation in English Language.
Suspected Iran-Linked Cyberattack Hits U.S. Medical Device Company.
Reports indicate that a cyberattack believed to be linked to Iran targeted U.S. medical technology company Stryker Corporation, marking what analysts say could be the first major cyber strike on an American firm since the ongoing conflict between Iran and the United States began.
Cybersecurity experts say a hacking group known as Handala hacking group claimed responsibility, reporting that more than 200,000 devices were wiped and roughly 50 terabytes of data were stolen from the company’s systems.
Employees reported that company phones and laptops were disrupted, affecting internal communications globally.
Stryker Corporation confirmed a cybersecurity incident in parts of its internal systems but stated there was no clear evidence of ransomware or malware that could disrupt its medical products and services.
Security analysts warn that the incident could signal an expansion of the conflict into cyberspace, with attacks on private companies designed to exert economic and psychological pressure.
Investigations are ongoing to determine the full impact of the attack and whether there is any direct involvement of Iran authorities.

0 Comments:
Post a Comment