Ƙasar Sin Ta Zargi Amurka Da Haddasa Rikicin Batun Nukiliyar Iran.

Ƙasar Sin Ta Zargi Amurka Da Haddasa Rikicin Batun Nukiliyar Iran.

Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya bayyana cewa Amurka ce tushen matsalar da ake ciki a halin yanzu dangane da shirin nukiliyar Iran, yana mai cewa matakan da Amurka ta dauka sun saba wa dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin da ke kunshe cikin kundin tsarin United Nations.

Fu Cong ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin zaman kwamitin nazarin takunkuman da aka kakabawa Iran na Kwamitin tsaro na majalisar dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa kasar Sin na matukar adawa da matakan da Amurka ta dauka kan wannan batu.

News Translation in English Language.

China Blames US for Current Crisis Over Iran’s Nuclear Program.

China’s permanent representative to the United Nations, Fu Cong, has said that the United States is responsible for the current crisis surrounding Iran’s nuclear program, stressing that Washington’s actions violate international law and the principles enshrined in the charter of the United Nations.

Fu Cong made the remarks on Thursday during a meeting of the sanctions committee on Iran at the United Nations Security Council, where he reiterated that China strongly opposes the measures taken by the United States on the issue.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: