Rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran IRGC Ta Kai Hare-Hare Kan Sansanonin Sojin Isra’ila da na Amurka

Rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran IRGC Ta Kai Hare-Hare Kan Sansanonin Sojin Isra’ila da na Amurka

Rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, IRGC ta sanar da kaddamar da wani sabon babban farmaki da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki kan Sansanonin sojin Isra’ila da kuma na Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce harin wani bangare ne na jerin hare-haren ramuwar gayya da Iran ke ci gaba da kaiwa sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu muhimman wurare a cikin Iran a makonnin baya.

Sanarwar ta bayyana cewa an harba makamai masu linzami da dama da kuma jiragen sama marasa matuki zuwa wasu wuraren sojin Isra’ila, inda aka ce an kai hari kan cibiyoyi da sansanonin soji da ake amfani da su wajen kai farmaki kan Iran.

Har ila yau, rundunar ta ce wasu sansanonin sojin Amurka da ke yankin ma sun fuskanci hare-haren, ciki har da sansanonin da ke Bahrain da kuma Erbil a Iraki.

IRGC ta kara da cewa wannan farmaki wani sabon mataki ne a cikin hare-haren da take kira “Operation True Promise”, wanda aka kaddamar domin mayar da martani ga hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan kasar Iran.

Rikicin da ke tsakanin Iran da kasashen biyu ya kara tsananta a kwanakin baya, inda bangarorin ke ci gaba da musayar hare-hare, lamarin da ke haifar da fargabar kara fadada rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni daga kafofin yada labarai sun nuna cewa wannan sabon harin na daga cikin jerin hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kaiwa tun bayan barkewar rikicin, wanda ya haddasa tashin hankali a kasashe da dama na yankin.

News Translation in English Language.

IRGC Launches Major Strikes on Israeli Military Sites and U.S. Bases.

Tehran, Iran — The Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) has announced a major new offensive using ballistic missiles and unmanned aerial vehicles targeting Israeli military sites and U.S. bases across the Middle East.

According to the IRGC statement, the attacks are part of ongoing retaliatory operations in response to earlier strikes by the United States and Israel on strategic locations inside Iran.

The statement said multiple ballistic missiles and drones were launched toward Israeli military installations, including key bases and operational centers used in attacks against Iran.

Additionally, several U.S. bases in the region were reportedly targeted, including facilities in Bahrain and Erbil, Iraq.

The IRGC described the offensive as a new phase in “Operation True Promise”, intended as retaliation for the joint U.S.-Israeli strikes.

The conflict between Iran and the two nations has intensified in recent days, with both sides continuing to exchange attacks, raising fears of further escalation across the Middle East.

Media reports indicate that this latest operation is part of a series of missile strikes Iran has conducted since the outbreak of hostilities, which have already caused widespread tension across multiple regional countries.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: