Dubban Iraniyawa sun taru Domin gudanar da gangamin tunawa da ranar Qudus ta Duniya.

Dubban Iraniyawa sun taru Domin gudanar da gangamin tunawa da ranar Qudus ta Duniya.

Yadda Dubun-dubatan mutane suka taru a birnin Tehran na ƙasar Iran domin gudanar da gangamin tunawa da Ranar Qudus ta duniya, a daidai lokacin da rikicin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ke dab da cika makonni biyu.

Masu zanga-zangar sun fito kan tituna suna nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu tare da yin Allah wadai da Isra’ila, yayin da ake ci gaba da tashin hankali a yankin.

Ranar Al-Quds wata rana ce ta shekara-shekara da ake gudanar da ita a ranar Juma’a ta ƙarshe a watan azumin Ramadan, domin nuna goyon baya ga Falasdinu da kuma nuna adawa da mamayar Isra’ila a yankunan Falasdinawa. 
An kafa wannan rana ne a shekarar 1979 ta hannun jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ruhollah Khomeini. 

A kowace shekara, Iran da wasu ƙasashe na Musulmi kan shirya manyan taruka da gangami domin wannan rana, inda ake kira ga haɗin kan Musulmi wajen goyon bayan Falasdinu da kuma neman ‘yantar da birnin Kudus. 

Gangamin na bana ya zo ne a lokacin da rikicin da ya barke a yankin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta, inda hare-haren juna tsakanin Iran da Isra’ila da ƙawayenta ke ci gaba, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama tare da tayar da hankulan duniya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: