Sabon Jagoran Juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya gabatar da jawabinsa na farko ga al’ummar ƙasar bayan nada shi a matsayin Jagoran Kolin kasar, inda ya yi kira ga ƙarfafa haɗin kai da tsayin daka a tsakanin ‘yan Iran a wannan lokaci na yaƙi da ƙasar ke fuskanta.
A cikin sakon da aka wallafa yau Alhamis, Mojtaba Khamenei ya bayyana alhini kan rasuwar mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu a kwanakin baya sakamakon hare-haren hadin gwiwar Israi'la da Amurka da suka auka wa ƙasar.
Sabon jagoran ya bukaci al’ummar Iran da su kasance cikin haɗin kai, juriya da sadaukarwa, yana mai cewa wannan lokaci na bukatar dukkan ‘yan ƙasa su tsaya tsayin daka domin kare martaba da ‘yancin kai na ƙasarsu.
Mojtaba Khamenei ya jaddada cewa al’ummar Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare ƙasar su daga duk wata barazana, yana mai cewa Iran za ta ci gaba da bin manufofinta na kare muradun ƙasa da martabar al’ummarta.
Hakazalika, ya yi nuni da cewa Iran za ta ci gaba da tsayawa kan matsayinta dangane da rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da yin kira ga ‘yan ƙasar su kasance cikin shiri da haɗin kai domin fuskantar kalubalen da ke gaba.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan sakon na farko da Mojtaba Khamenei ya fitar yana nuni da cewa sabon jagoran zai ci gaba da tafiyar da manufofin siyasa da tsaron ƙasa irin na gwamnatin da ta gabata, musamman wajen tsayawa tsayin daka kan batutuwan da suka shafi ikon ƙasa da rikicin yankin.
News Translation in English Language.
Iran’s New Leader Calls for National Unity in First Message.
Iran’s new Supreme Leader, Mojtaba Khamenei, has issued his first message to the nation after assuming leadership, calling on Iranians to strengthen national unity and remain steadfast amid the challenges facing the country.
In a statement released on Thursday, Mojtaba Khamenei expressed deep sorrow over the death of his father, former Iranian Supreme Leader Ali Khamenei, who recently died following attacks on the country.
The new leader urged the Iranian people to maintain strong solidarity, patience, and sacrifice during what he described as a critical period for the nation. He said the moment requires all citizens to stand together in order to protect Iran’s independence, dignity, and national interests.
Mojtaba Khamenei also stressed that the Iranian people would not retreat from defending their country against any threats. According to him, Iran will continue to pursue its policies aimed at safeguarding its sovereignty and the rights of its people.
He further indicated that Iran would maintain its stance regarding the ongoing tensions in the Middle East, urging citizens to remain united and prepared to face the challenges ahead.
Political analysts say the message suggests that Mojtaba Khamenei is likely to continue many of the policies of the previous leadership, particularly Iran’s firm position on national security and regional issues.

0 Comments:
Post a Comment