Wata kotun soja a birnin Moscow ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutane 15 da aka same su da laifin kai harin ta’addanci a Crocus City Hall a ranar 22 ga Maris, 2024, wanda ya kashe kimanin mutane 150 kuma ya jikkata daruruwan wasu.
Hukuncin ya hada da:
Mutane 15 an yanke musu hukuncin rai da rai a gidan yari.
Wani mutum ya samu hukuncin shekaru 22 da rabi, yayin da sauran mutum 3 suka samu shekaru kusan 20 a gidan yari.
Binciken kotu ya nuna cewa manyan masu kai harin, 'yan ƙasar Tajikistan ne, Inda suka bude wuta a kan masu halartar taron kuma suka kunna wuta a cikin dakin wasan.
Sauran wadanda aka yanke wa hukunci sun hada da wadanda aka samu da hannu wajen taimaka wa masu kai harin, kamar sayar da motarsu da hayan gidan zama, ko samun alaka da ta’addanci.
Harin na 2024 ya kasance mafi muni a Moscow cikin shekaru sama da goma, inda kungiyar ta’addanci mai alaka da IS-Khorasan ta dauki alhakin kai harin.
Wannan lamari ya janyo karuwar matakan tsaro a birnin Moscow da kuma muhawara kan yadda za a yaki ta’addanci a cikin Rasha.
News Translation in English Language.
Russia Sentences 15 to Life Imprisonment Over 2024 Moscow Crocus City Hall Attack.
A military court in Moscow has sentenced 15 individuals to life imprisonment for their involvement in the terrorist attack at Crocus City Hall on March 22, 2024, which killed approximately 150 people and injured hundreds more.
The court rulings are as follows:
15 people received life sentences in prison.
One individual was sentenced to 22½ years, while three others received nearly 20-year prison terms.
Investigations revealed that the main perpetrators were Tajik nationals who opened fire on attendees and set off explosives inside the venue. Other convicted individuals were found to have assisted the attackers, such as providing vehicles, housing, or other forms of logistical support linked to terrorism.
The 2024 attack was the deadliest in Moscow in over a decade, claimed by the IS-Khorasan affiliate. The incident prompted heightened security measures across Moscow and sparked renewed debates on counter-terrorism strategies in Russia.

0 Comments:
Post a Comment