Wani jirgin ruwan dakon Mai ya Kama da Wuta a gabar tekun Iraqi bayan Iran Ta kai mashi hari.

Wani jirgin ruwan dakon Mai ya Kama da Wuta a gabar tekun Iraqi bayan Iran Ta kai mashi hari.

Wani jirgin ruwan dakon mai mallakin ƙasashen turai da ke ɗauke da man fetur na Iraki ya kama da wuta a tekun Iraki bayan wani hari da ake zargin Iran ce ta kai. 
Wannan na zuwa ne a cikin sabon jerin hare-hare kan cibiyoyin mai da sufuri a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun ce harin na daga cikin rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Iran da hadakar Amurka da Isra’ila. 
Iran ta kuma yi gargadin cewa duniya ta shirya, domin farashin mai na iya haura dala $200 kan kowace ganga idan rikicin ya ci gaba.

Yaƙin ya ɓarke ne kusan makonni biyu da suka wuce bayan hare-haren sama na haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran. 
Tun daga lokacin, rikicin ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 2,000, tare da jefa kasuwannin makamashi na duniya da harkokin sufuri cikin rudani.

Rikicin ya bazu zuwa sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya sa ƙasashe da dama suka fara shirin sakin adadin mai daga ajiyar gaggawa (strategic oil reserves) domin rage tasirin tashin farashin mai, wanda ake ganin zai iya zama ɗaya daga cikin mafi muni tun bayan rikicin man fetur na shekarun 1970.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: