Adadin Mutanen da Suka Jikkata a Hare-Haren da Iran ta kai Isra'ila Sun Kusa mutum 3,000.

Adadin Mutanen da Suka Jikkata a Hare-Haren da Iran ta kai Isra'ila Sun Kusa mutum 3,000.

Rahotanni daga hukumomin lafiya na Israi'la sun bayyana cewa adadin mutanen da suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da Iran ta kai kan ƙasar ya kusa kaiwa mutum 3,000, yayin da aƙalla mutane 13 suka mutu tare da haddasa babbar barna a wasu yankunan ƙasar.

An ce da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata sun samu raunuka ne yayin da suke gudu zuwa wuraren kariya (shelters) bayan ƙararrawar gargadin harin makamai ta tashi a birane da dama ciki har da Tel Aviv da sauran yankunan tsakiyar ƙasar. 

Hare-haren na Iran sun zo ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila tare da Amurka suka kai wa wasu wurare a Iran, wanda ya haifar da rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya. 

Masana harkokin tsaro na duniya sun yi gargadin cewa rikicin na iya ƙara tsananta idan ba a samu hanyar sulhu tsakanin ɓangarorin da ke rikicin ba, domin yaƙin ya riga ya jawo asarar rayuka da barnar dukiya a ƙasashe da dama na yankin.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: