Ba zamu dakatar da yaƙi da Israi'la da Amurka ba har sai an aminta da sharuɗɗa uku - Masoud Pezeshkian.

Ba zamu dakatar da yaƙi da Israi'la da Amurka ba har sai an aminta da sharuɗɗa uku - Masoud Pezeshkian.

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce Iran ba za ta amince da kawo ƙarshen yaƙin ta da Israi'la da Amurka ba sai an amince da haƙƙoƙinta da kuma ɗaukar matakin da ya dace kan abin da ya kira hare-haren da aka kai wa ƙasar.

Inda ya bayyana cewa za a iya kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Amurka da Isra’ila ne kawai idan aka cika wasu muhimman sharudda uku da ƙasar ta gindaya.

A cewar jami’an Iran, sharuddan da suka gindaya sun haɗa da:

Na farko, dole ne Amurka da Isra’ila su amince da haƙƙin Iran na siyasa da na tsaro, ciki har da ‘yancin ta na ci gaba da shirye-shiryenta na fasaha da kariyar ƙasa.

Na biyu, Iran na buƙatar a biya ta diyya kan asarar da ta jikkata sakamakon hare-haren da aka kai mata, ciki har da lalacewar gine-gine da kuma asarar rayukan fararen hula.

Na uku, Iran ta ce wajibi ne ƙasashen da ta zarga da fara wannan rikici su ɗauki alhakin abin da ya faru, tare da amincewa da sakamakon yaƙin.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaƙi, amma ba za ta yi shiru ba idan aka ci gaba da kai mata hari.

Rikicin tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila ya ƙara kamari a kwanakin baya, bayan da aka kai hare-hare kan wasu wurare a Iran, lamarin da ya haifar da mayar da martani daga Iran ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa wasu wurare a yankin Gabas ta Tsakiya.

Masana harkokin tsaro na gargadi cewa rikicin na iya ƙara tsananta idan ba a samu hanyar sasanci ba tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.

News Translation in English Language.

Iran Will Not End War With Israel and U.S. Until Three Conditions Are Met – Masoud Pezeshkian.

Iran’s President, Masoud Pezeshkian, has declared that Iran will not agree to end its conflict with Israel and the United States unless the country’s rights are recognized and appropriate action is taken over what he described as attacks against Iran.

He stated that the war between Iran, the United States, and Israel could only come to an end if three key conditions set by Iran are fulfilled.

According to Iranian officials, the conditions include:

First, the United States and Israel must recognize Iran’s political and security rights, including its right to continue its technological programs and national defense initiatives.

Second, Iran is demanding compensation for the damages it suffered as a result of the attacks carried out against the country, including destruction of infrastructure and the loss of civilian lives.

Third, Iran insists that the countries it accuses of initiating the conflict must accept responsibility for what happened and acknowledge the consequences of the war.

President Pezeshkian emphasized that Iran is not seeking war, but will not remain silent if attacks against the country continue.

Tensions between Iran, the United States, and Israel have escalated in recent days following strikes on several locations inside Iran. The attacks reportedly prompted retaliation from Iran, which launched missiles and drones targeting locations across the Middle East.

Security analysts have warned that the conflict could intensify further if diplomatic efforts fail to produce a resolution between the parties involved.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: