Gwamnatin Trump Ta Ce Yakin Amurka da Iran Ya Ci Sama da Dala Biliyan 11 Cikin Kwana Shida kacal.

Gwamnatin Trump Ta Ce Yakin Amurka da Iran Ya Ci Sama da Dala Biliyan 11 Cikin Kwana Shida kacal.

Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump, ta bayyana cewa hare-haren soji da Amurka ta kaddamar kan Iran sun ci makudan kudade, inda aka kiyasta cewa sama da dala biliyan 11.3 aka kashe cikin kwanaki shida na farkon yakin.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin kwanaki biyu na farko kawai, Amurka ta kashe kimanin dala biliyan 5.6 wajen amfani da makamai masu linzami da sauran manyan makamai da aka harba a wurare da dama a Iran.

A cewar jami’an Pentagon, mafi yawan kudin da aka kashe ya tafi ne wajen harba makamai masu tsada kamar Tomahawk cruise missiles da sauran manyan makaman kai hari. Wannan mataki ya jawo damuwa a Majalisar Dokokin Amurka saboda yiyuwar raguwar ajiyar makaman sojin kasar.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa saurin kashe irin wadannan kudade na iya haifar da matsin lamba ga tattalin arzikin Amurka, musamman ma idan yakin ya dauki lokaci mai tsawo. Haka kuma wasu ‘yan majalisar dokoki sun bukaci gwamnati ta fito fili ta bayyana dalilin yakin da kuma irin kudaden da za a ci gaba da kashewa.

A gefe guda, yakin ya fara haifar da wasu matsaloli na tattalin arziki, ciki har da tashin farashin mai da kuma damuwar siyasa a cikin Amurka, yayin da ake sa ran gwamnatin Trump za ta nemi karin kudade daga Majalisa domin ci gaba da ayyukan soji.

Masana suna gargadin cewa idan wannan yanayi ya ci gaba, kudin yakin na iya kaiwa biliyoyin daloli a kowane mako, musamman idan rikicin ya kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

News Translation in English Language.

Trump Administration Says U.S.-Iran War Cost Over $11 Billion in First Six Days.

The administration of U.S. President Donald Trump has revealed that military operations against Iran have already incurred massive costs, with estimates exceeding $11.3 billion in the first six days of the conflict.

Reports indicate that in just the first two days alone, the United States spent approximately $5.6 billion on missiles and other advanced weaponry fired at multiple locations across Iran.

According to Pentagon officials, most of the spending went toward expensive armaments such as Tomahawk cruise missiles and other major strike weapons. Lawmakers have expressed concern over the potential depletion of U.S. military stockpiles.

Security analysts warn that such rapid expenditure could put pressure on the U.S. economy, especially if the conflict is prolonged. Some members of Congress have called on the administration to provide transparency regarding the reasons for the war and ongoing costs.

Meanwhile, the conflict has already contributed to economic challenges, including rising fuel prices and domestic political concerns, as the Trump administration is expected to seek additional funds from Congress to continue military operations.

Experts caution that if the situation continues, the war could cost billions of dollars per week, particularly if tensions escalate further in the Middle East.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: