EFCC Ta Sake Gurfanar da Akanta Janar na jihar Bauchi a Kotu Kan Zargin Badakalar N1.48bn.

EFCC Ta Sake Gurfanar da Akanta Janar na jihar Bauchi a Kotu Kan Zargin Badakalar N1.48bn.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta sake gurfanar da Babban Akanta na Jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin hannu a badakalar kuɗi da suka kai Naira biliyan 1.48. 

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da Jaja tare da wani ɗan kasuwa mai harkar canjin kuɗi, Aliyu Abubakar, da kuma kamfaninsa mai suna Jasfad Resources Enterprise a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu. 

EFCC ta zarge su da aikata laifuffuka da suka haɗa da karkatar da kuɗin gwamnati da halasta kuɗaɗen haram, inda ake zargin sun tura kuɗaɗen gwamnati zuwa asusun wani kamfani domin amfanin kansu. 

A cewar takardun tuhumar da aka gabatar a kotu, ana zargin cewa daga Oktoba zuwa Disamba 2024 an cire sama da Naira biliyan 1.19 daga asusun gwamnatin jihar Bauchi aka tura su zuwa asusun kamfanin Jasfad. Haka kuma an ce daga Janairu zuwa Maris 2025 an sake karkatar da Naira miliyan 296 zuwa wannan asusu. 

Hukumar EFCC ta kuma bayyana wasu mutane uku da take nema ruwa a jallo dangane da badakalar, ciki har da Abubakar Muhammad Hafiz da Ari Manga da Muhammad Aminu Bose. 

Sai dai waɗanda ake tuhuma sun musanta dukkan zarge-zargen, yayin da lauyoyinsu suka roƙi kotu ta bar su su ci gaba da cin gajiyar belin da aka ba su a baya, wanda kotun ta amince da shi. 

News Translation in English Language.

Trump Administration Says U.S.-Iran War Cost Over $11 Billion in First Six Days.

The administration of U.S. President Donald Trump has revealed that military operations against Iran have already incurred massive costs, with estimates exceeding $11.3 billion in the first six days of the conflict.

Reports indicate that in just the first two days alone, the United States spent approximately $5.6 billion on missiles and other advanced weaponry fired at multiple locations across Iran.

According to Pentagon officials, most of the spending went toward expensive armaments such as Tomahawk cruise missiles and other major strike weapons. Lawmakers have expressed concern over the potential depletion of U.S. military stockpiles.

Security analysts warn that such rapid expenditure could put pressure on the U.S. economy, especially if the conflict is prolonged. Some members of Congress have called on the administration to provide transparency regarding the reasons for the war and ongoing costs.

Meanwhile, the conflict has already contributed to economic challenges, including rising fuel prices and domestic political concerns, as the Trump administration is expected to seek additional funds from Congress to continue military operations.

Experts caution that if the situation continues, the war could cost billions of dollars per week, particularly if tensions escalate further in the Middle East.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form