‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 14, tare da Jikkata wasu da Dama a Sabbin Hare-Hare a Jihar Katsina.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 14, tare da Jikkata wasu da Dama a Sabbin Hare-Hare a Jihar Katsina.

Akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a wasu al’ummomi na Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne a ƙananan hukumomin Dandume da Musawa, inda maharan suka kutsa cikin wasu ƙauyuka tare da bude wuta kan mazauna yankunan.

Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun iso da yawa dauke da makamai, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu.

An kuma ce wasu daga cikin waɗanda suka samu raunuka an garzaya da su asibitocin da ke kusa domin samun kulawar likitoci.

A daya daga cikin hare-haren, maharan sun kai farmaki a garin Jikamshi da ke karamar hukumar Musawa, inda rahotanni suka tabbatar da cewa an samu asarar rayuka da kuma jikkatawar wasu mazauna yankin.

Jami’an tsaro sun yi Allah wadai da hare-haren tare da bayyana cewa ana kokarin farautar wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban doka.

Sabbin hare-haren na kara jaddada barazanar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke yawan kai hare-hare kan kauyuka tare da kashe mutane ko kuma su sace su domin neman kudin fansa.

News Translation in English Language.

Bandit Attacks in Katsina Leave 14 Dead, Several Injured.

At least 14 people have been killed and several others injured following fresh attacks by armed bandits in communities across Katsina State.

Reports indicate that the attacks took place in the Dandume and Musawa Local Government Areas, where gunmen stormed villages and opened fire on residents.

Eyewitnesses said the attackers arrived in large numbers, armed with weapons, indiscriminately targeting civilians, resulting in multiple deaths and injuries. Some of the wounded were reportedly rushed to nearby hospitals for medical treatment.

In one incident, bandits attacked Jikamshi town in Musawa LGA, with security sources confirming casualties and injuries among residents.

Security agencies have condemned the attacks and are said to be working to track down the perpetrators for prosecution.

The latest incidents highlight the ongoing banditry crisis in northwestern Nigeria, where armed groups frequently raid villages, kill civilians, and carry out kidnappings for ransom.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form