Kasashe takwas na Musulmi sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na ci gaba da rufe ƙofofin Masallacin Al-Aqsa ga masu ibada Musulmi, musamman a lokacin watan Ramadan.
Ministocin harkokin wajen kasashen sun hada da:
Saudi Arabia
Masar
Jordan
Hadaddiyar daulan Larabawa (UAE)
Qatar
Turkiya
Indonesiya
Pakistan
Sun bayyana cewa hana Musulmi shiga harabar masallacin da ke cikin tsohon birnin Jerusalem ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma tsarin tarihi da na shari’a da aka dade ana bi wajen kula da wuraren ibada.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa Isra’ila ba ta da ikon mallakar Gabashin Jerusalem ko wuraren ibada na Musulmi da Kiristoci da ke cikinta. Kasashen sun yi kira ga Isra’ila da ta bude ƙofofin masallacin nan bada jimawa ba tare da barin masu ibada su shiga cikin ‘yanci.
Har ila yau, ministocin sun bukaci kasashen duniya su dauki mataki mai karfi domin dakatar da abin da suka kira cin zarafin wuraren ibada da ke birnin Jerusalem.
Masallacin Al-Aqsa shi ne wuri na uku mafi tsarki ga Musulmi a duniya, kuma yana cikin tsohon birnin Jerusalem.
News Translation in English Language.
Eight Arab and Islamic Countries Condemn Israel’s Continued Closure of Al-Aqsa Mosque Gates.
Eight Arab and Islamic nations have jointly condemned Israel’s ongoing closure of the gates of Al-Aqsa Mosque in Jerusalem, calling the move a violation of international law and historical agreements regarding access to holy sites.
The countries involved in the joint statement are:
Saudi Arabia
Egypt
Jordan
United Arab Emirates
Qatar
Türkiye
Indonesia
Pakistan
The ministers emphasized that restricting Muslim worshippers from entering the mosque, especially during Ramadan, breaches legal and religious norms and undermines the sanctity of the site. The statement underlined that Israel has no sovereign claim over East Jerusalem or the Islamic and Christian holy sites within it.
The eight nations also urged the international community to take firm action to stop violations against places of worship in Jerusalem and called on Israel to immediately reopen Al-Aqsa Mosque gates to worshippers.
Al-Aqsa Mosque, located in Jerusalem’s Old City, is the third holiest site in Islam and a focal point of religious and political tensions in the region.
Tags
Labarai
