Hare-Haren Ramuwar Gayya da Iran ta kai ya hallaka sojojin Amurka, Tare da Lalata Sansanonin Soja 17 a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hare-Haren Ramuwar Gayya da Iran ta kai ya hallaka sojojin Amurka, Tare da Lalata Sansanonin Soja 17 a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun mutu yayin da aƙalla sansanonin soja 17 na Amurka suka lalace sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a wasu Ƙasashe a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Press TV ta ruwaito, hare-haren sun kasance martani ne ga matakan soji da Amurka da kuma Israel suka ɗauka kan wasu muhimman wurare a cikin Iran.

Rahoton ya ce an kai hare-haren ne ta amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, inda aka nufi wuraren da sojojin Amurka ke da sansanoni ko muhimman kayayyakin soja a ƙasashe daban-daban na yankin.

Rahotan ya ce, Hare-haren sun shafi sansanonin soja na Amurka da ke ƙasashe kamar Iraq da Jordan da Kuwait da kuma Bahrain.

Sai dai har yanzu hukumomin Amurka ba su fitar da cikakken bayani kan yawan asarar rayuka da aka samu ba, yayin da rahotanni ke cewa akwai sojojin da suka jikkata sakamakon hare-haren.

Masu sa ido kan harkokin tsaro sun bayyana cewa wannan farmaki na iya ƙara tsananta rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Iran da Amurka tare da ƙawayenta, lamarin da ka iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin sabon yanayi na tashin hankali.

Rahotanni sun kuma nuna cewa rikicin na iya shafar harkokin tattalin arziki na duniya, musamman jigilar man fetur ta mashigar Hormuz, wadda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci wajen jigilar mai a duniya.

News Translation in English Language.

Iran Says Retaliatory Strikes Kill US Troops, Damage 17 Military Sites Across Middle East.

Iran has claimed that several United States troops were killed and at least 17 American military sites were damaged in retaliatory attacks carried out across the Middle East.

According to a report by Press TV, the strikes were launched in response to military actions by the United States and Israel against targets inside Iran.

The report stated that the attacks involved missiles and unmanned aerial vehicles (drones), targeting locations where U.S. forces maintain military bases and strategic facilities across the region.

The retaliatory strikes reportedly affected American military positions in several countries, including Iraq, Jordan, Kuwait and Bahrain.

However, officials from the United States have not yet released detailed information regarding the number of casualties, although reports indicate that several troops were also injured during the attacks.

Security analysts say the strikes could further escalate tensions between Iran and the United States and its allies, raising concerns about a wider conflict across the Middle East.

Observers also warn that the growing confrontation could affect global energy markets, particularly shipping through the strategic Strait of Hormuz, one of the world’s most important routes for oil transportation.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form