Shugabannin kasashen Tarayyar Turai (EU) sun ki amincewa da kiran Shugaban Amurka, Donald Trump, na tura sojoji don tabbatar da ‘yancin zirga‑zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz yayin da yaƙi tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran ke kara tsananta.
A lokacin taron ministocin harkokin wajen EU a Brussels, sun jaddada cewa ƙasashen Turai ba sa son haɗa kansu cikin ayyukan soja a wannan rikici, inda Jamus da Sifaniya suka bayyana a fili za su guji irin wannan katsalandan.
Wannan ƙauracewar ya zo ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi tsokacin cewa ƙasashen da ke amfani da makamashi daga yankin Gulf su taimaka wajen tsare wannan mahimmiyar hanyar ruwa sakamakon hauhawar farashin mai a duniya.
A gefe guda, wasu ƙasashen duniya kamar Japan da Australia ma sun bayyana cewa ba za su tura jiragen ruwan sojin su don tabbatar da tsaron tashar ba, duk da kiran da Trump ya yi.
News Translation in English Language.
EU Leaders Reject Trump’s Call to Deploy Troops to Strait of Hormuz.
EU leaders have rejected U.S. President Donald Trump’s request to send troops to secure free navigation through the Strait of Hormuz, amid escalating tensions between the United States, Israel, and Iran.
During a meeting of EU foreign ministers in Brussels, officials emphasized that European countries do not want to involve themselves in military operations in this conflict, with Germany and Spain openly stating they will avoid such intervention.
This refusal comes after President Trump suggested that countries reliant on energy from the Gulf region should assist in securing this vital waterway due to rising global oil prices.
Meanwhile, other nations, including Japan and Australia, have also stated they will not deploy naval forces to protect the strait, despite Trump’s appeal.

0 Comments:
Post a Comment