Jirgin Ƙasa dake zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna ya yi hatsari.

Jirgin Ƙasa dake zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna ya yi hatsari.

Jirgin ƙasa da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna ya yi hatsari bayan ya sauka daga layin dogo, Inda wasu daga cikin fasinjojin suka samu raunuka tare janyo firgici a tsakanin mutanen da ke cikin jirgin.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin na kan hanyarsa ne ta zuwa Abuja daga Kaduna lokacin da wani ɓangare na jirgin ya kauce daga layin dogo, lamarin da ya sa jirgin ya girgiza ƙwarai tare da jefa wasu fasinjoji cikin firgici.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sun ji wani ƙara mai ƙarfi kafin jirgin ya yi wani irin jijjiga, wanda hakan ya sa wasu fasinjoji suka bugi kujeru ko kuma suka faɗi a cikin jirgin. 
Sakamakon haka, wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunuka kamar yanke-yanke da kuma kumburi a jiki.

Bayan aukuwar lamarin, an dakatar da tafiyar jirgin na ɗan lokaci domin a tantance abin da ya faru da kuma tabbatar da lafiyar fasinjojin da ke cikin jirgin.

Hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, wato Nigerian Railway Corporation, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin kwatsewar jirgin daga layin dogo.

Sai dai kawo yanzu babu rahoton mutuwa, yayin da jami’an agaji da na tsaro ke kula da fasinjojin da suka samu raunuka.

Rahotanni sun kuma nuna cewa an ɗauki matakan gaggawa domin dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa a kan layin na Abuja zuwa Kaduna bayan tantance halin da layin dogon yake ciki.

News Translation in English Language.

Passengers Injured as Abuja–Kaduna Train Derails.

Several passengers were injured after a train operating on the Abuja–Kaduna rail line derailed on Monday, causing panic among those on board.

Reports indicate that the train was travelling from Kaduna to Abuja when part of it suddenly left the rail track, leading to a violent jolt that alarmed passengers.

Eyewitnesses said they heard a loud bang before the train began shaking heavily, forcing some passengers to hit their seats or fall inside the coach. As a result, several passengers sustained injuries, including cuts and bruises.

Following the incident, the train was forced to stop temporarily along the rail corridor while authorities assessed the situation and ensured the safety of passengers.

Officials from the Nigerian Railway Corporation confirmed the incident and stated that investigations are ongoing to determine the exact cause of the derailment.

However, no deaths had been reported as of the time of filing this report. Emergency responders and security personnel were said to be attending to injured passengers.

Authorities also said necessary steps were being taken to restore normal train operations along the Abuja–Kaduna route after safety checks on the rail line.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: