Aƙalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da 100 suka jikkata sakamakon jerin hare-haren kunar bakin wake da suka auku a birnin Maiduguri na Jihar Borno.
Hare-haren, wadanda ake zargin masu kai su ‘yan kunar bakin wake ne, sun faru ne da yammacin ranar Litinin a wurare daban-daban, ciki har da kofar Asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri, da kuma kasuwannin Post Office da Kasuwar litini (Monday Market).
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa binciken farko ya nuna cewa ‘yan kunar bakin wake ne suka kai hare-haren.
“Abin takaici, jimillar mutane 23 sun mutu, yayin da 108 suka samu raunuka daban-daban,” in ji shi.
A nasa bangaren, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) a Maiduguri, Surajo Abdullahi, ya ce ana kula da wadanda suka jikkata a asibitoci daban-daban a birnin.
Ya bayyana cewa, mutane 108 na karɓar magani a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri, yayin da 20 ke asibitin Umaru Shehu, sai kuma 17 a Maiduguri Specialist Hospital.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin, tare da daukar matakan tsaro domin kauce wa sake aukuwar irin wannan hari.
Wannan hari ya sake nuna irin barazanar tsaro da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke fuskanta duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen dakile ayyukan ta’addanci.
News Translation in English Language.
At Least 23 Killed in Suicide Bombings in Maiduguri.
At least 23 people have been killed and more than 100 injured in a series of suspected suicide bombings in Maiduguri, Borno State.
The attacks occurred on Monday evening at multiple locations, including the entrance of the University of Maiduguri Teaching Hospital, the Post Office market, and the Monday Market. Authorities believe the bombings were carried out by suicide attackers.
> “Tragically, a total of 23 people have died, while 108 others sustained various injuries,” said Nahum Kenneth Daso, the state police spokesperson.
The National Emergency Management Agency (NEMA) in Maiduguri confirmed that the injured are receiving treatment at multiple hospitals across the city. 108 patients are being treated at the University Teaching Hospital, 20 at Umaru Shehu Hospital, and 17 at Maiduguri Specialist Hospital.
Authorities are continuing investigations to determine full details of the attack and are implementing additional security measures to prevent further incidents.
The attack highlights the ongoing security challenges in northeastern Nigeria despite ongoing efforts by security forces to combat terrorism.

0 Comments:
Post a Comment