Ministocin ƙasashen larabawa da na Musulmi Suna taro a birnin Riyadh domin Tattauna Matakan Tsaro Kan Hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kaiwa a Kasashen yankin gabas ta tsakiya, lamari dake kara dagula tsaro a yankin.
Taron ya biyo bayan harin Iran da ya shafi manyan wuraren makamashi a Saudiya da UAE da Qatar, wanda Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin Isra’ila a filin gas na South Pars, babban tushen makamashi na Iran.
Ministocin sun yi Allah wadai da hare-haren Iran na amfani da makaman roka da jiragen sama marasa matuki, wanda ya shafi gidaje da tashoshin ruwa da masana’antu da filayen jiragen sama da ofisoshin diflomasiyya. Sun kuma jaddada haƙƙin ƙasashen na kare kan su bisa ga Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya, Babban Sashe na 51.
Sun bukaci Iran da ta:
Dakatar da hare-harenta.
Tsayar da duk wata aikin tashin hankali ko barazana ga makwabta.
Daina tallafawa, hada-hadar kudi da bayar da makamai ga ƙungiyoyin proxy da ke aiki a ƙasashen Arab.
Kaucewa matakai ko barazanar da ke shafar tsaron teku, musamman a Strait of Hormuz da Bab al-Mandeb.
Haka kuma, ministocin sun yi Allah wadai da hare-haren Isra’ila a Lebanon da manufofin fadada iko da aka gani a yankin.
Ministan harkokin wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud, ya nuna cewa Saudi Arabia da sauran ƙasashen yankin Gulf za su iya daukar mataki idan an buƙata, amma ya yi gargadi cewa zaman lafiya da Iran zai ɗauki lokaci saboda amewar da aka samu a dangantaka.
Taron ya haɗa ministoci daga Qatar da Azerbaijan da Bahrain da Egypt, Jordan da Kuwait da Lebanon da Pakistan da Saudi Arabia da Syria da Turkiye da UAE.
News Translation in English Language.
Arab and Muslim Ministers Hold Emergency Meeting in Riyadh on Iran Threats.
Arab and Muslim foreign ministers convened in Riyadh, Saudi Arabia to discuss security measures in response to retaliatory attacks by Iran across the Middle East, escalating regional tensions.
The meeting followed Iranian strikes targeting major energy facilities in Saudi Arabia, the UAE, and Qatar, carried out in retaliation for an Israeli strike on Iran’s South Pars gas field, one of the country’s primary energy sources.
Ministers condemned Iran’s use of missiles and drones, which affected residential areas, ports, industrial facilities, airports, and diplomatic offices. They also reaffirmed the right of states to defend themselves under Article 51 of the United Nations Charter.
The ministers called on Iran to:
Cease all attacks immediately.
Stop any acts of aggression or threats against neighboring countries.
End support, funding, or arming of proxy groups operating in Arab states.
Avoid actions or threats endangering maritime security, particularly in the Strait of Hormuz and Bab al-Mandeb.
They also condemned Israeli attacks in Lebanon and the broader expansionist policies seen in the region.
Saudi Foreign Minister Faisal bin Farhan Al Saud emphasized that Saudi Arabia and other Gulf states could take necessary measures if required, while warning that achieving peace with Iran will take time due to strained relations.
The meeting brought together ministers from Qatar, Azerbaijan, Bahrain, Egypt, Jordan, Kuwait, Lebanon, Pakistan, Saudi Arabia, Syria, Turkey, and the UAE.

0 Comments:
Post a Comment