Yadda fitaccen Malamin Addinin musulunci a Sokoto, Sheikh Musa Lukuwa, Ya Gudanar da Sallar Idi Duk da Umarnin Sarkin Musulmi na rashin ganin jinjirin watan Shawwal.

Sheikh Musa Lukuwa, Ya Gudanar da Sallar Idi

Yadda fitaccen Malamin Addinin musulunci a Sokoto, Sheikh Musa Lukuwa, Ya Gudanar da Sallar Idi Duk da Umarnin Sarkin Musulmi na rashin ganin jinjirin watan Shawwal.

Sheikh Musa Lukuwa, ya gudanar da Sallar Idin ne tare da mabiyansa, yana mai cewa ya dogara ne da sahihan rahotannin ganin wata daga ƙasar Jamhuriyar Nijar.

Ya bayyana cewa kasancewar Nijar ƙasa ce makwabta da Sokoto, akwai dalilin amincewa da rahotannin ganin wata daga can, kamar yadda ake karɓar irin waɗannan rahotanni daga wasu yankuna.

Malamin ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga fahimtarsa ta addini, ba wai don ƙalubalantar hukuncin Sarkin Musulmi ba. Ya ce idan aka tabbatar da ganin wata, wajibi ne a bi koyarwar addini.

A al’ada, Sarkin Musulmi shi ne jagoran da Musulmai a Najeriya ke bi wajen sanar da fara da kuma ƙarshen azumin Ramadan, domin tabbatar da haɗin kai. Sai dai a wasu lokuta, bambancin fahimta kan batun ganin wata kan haifar da sabani wajen gudanar da bukukuwan Sallah a wasu yankuna.

News Translation in English Language.

Sokoto Cleric Leads Eid Prayer Despite Sultan’s Directive on Moon Sighting

A prominent Islamic cleric in Sokoto, Sheikh Musa Lukuwa, conducted the Eid prayer with his followers despite the directive of the Sultan of Sokoto that the crescent moon of Shawwal had not been sighted.

Sheikh Lukuwa explained that his decision was based on credible reports confirming the sighting of the moon in the Republic of Niger.

He noted that Niger, being a neighboring country to Sokoto, provides a reasonable basis for accepting such moon-sighting reports, similar to how reports from other regions are sometimes recognized.

The cleric emphasized that his action was guided by his religious understanding and not intended to challenge the authority of the Sultan. According to him, once the moon sighting is verified, it becomes obligatory to act in accordance with Islamic teachings.

Traditionally, the Sultan of Sokoto serves as the spiritual leader for Muslims in Nigeria, responsible for officially announcing the beginning and end of Ramadan to ensure unity among the faithful. However, differences in interpretation regarding moon sighting occasionally lead to disagreements over the timing of Eid celebrations in some areas.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: