An Saki wani Mutum Bayan shafe Shekaru 19 a Kurkuku Saboda da laifin Fashin da ba shi ya aikata ba.

An Saki wani Mutum Bayan shafe Shekaru 19 a Kurkuku Saboda da laifin Fashin da ba shi ya aikata ba.

An saki wani mutum mai shekaru 61, mai suna Kenneth Windley, bayan ya shafe shekaru 19 a kurkuku kan wani fashi da ba shi da hannu a ciki.

Windley ya samu ‘yanci ne daga kotun Brooklyn a Jihar New York na Amurka, bayan masu gabatar da kara sun amince cewa sabbin shaidu sun tabbatar da rashin laifinsa.

An same shi da laifin fashi a shekarar 2007 wanda ya shafi kimanin dala 550, inda aka yi masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari saboda laifuffukan baya da ya taba yi. Duk da haka, Windley ya kasance yana ikirarin cewa ba shi da laifi.

Shari’ar da aka yi masa ta dogara ne sosai kan bayyana wanda abin ya faru da hujjojin da ba kai tsaye ba. 
Windley ya bayyana cewa bai sani ba cewa ya sayi takardar kudi da aka sata daga wasu abokansa, yana tsammanin cewa takardar kudin ta halal ce.

Bincike na baya-bayan nan ya gano sabbin shaidu, ciki har da ikirarin wasu mutane biyu da suka shiga irin waɗannan fashi, wanda ya tabbatar da ikirarin da Windley ke yi tun farko. 
Wannan ya sa masu gabatar da kara da lauyoyinsa suka nemi a soke hukuncinsa.

Bayan an sake shi, Windley ya nuna farin ciki, yana mai cewa wannan lamari ya kashe kusan shekaru ashirin na rayuwarsa, amma yana godiya cewa an gyara kuskuren a ƙarshe.

Babban Lauyan Jihar Brooklyn, Eric Gonzalez, ya kuma amince cewa shari’ar bai kamata ta faru ba tare da bada hakuri ga Windley kan hukuncin da ba shi ya aikata laifin ba.

Wannan lamari ya nuna damuwar da ake da ita game da hukuncin da ba daidai ba da kuma muhimmancin cikakken bincike da sake duba shari’u a tsarin shari’a.

News Translation in English Language.

Man Released After 19 Years in Prison for Robbery He Didn't Commit.

A 61-year-old man, Kenneth Windley, has been released after spending 19 years in prison for a robbery he did not commit.

Windley was freed by a Brooklyn court in New York, USA, after prosecutors acknowledged that new evidence proved his innocence.

He had been convicted in 2007 for a robbery involving approximately $550 and was sentenced to 20 years in prison due to prior offenses. However, Windley consistently maintained that he was not guilty.

The case had heavily relied on circumstantial evidence and witness statements. Windley stated that he was unaware that he had purchased a stolen money order from friends, believing it to be legitimate.

Recent investigations uncovered new witnesses, including two individuals involved in similar robberies, which confirmed Windley’s original claims. This led prosecutors and his lawyers to request the overturning of his conviction.

Upon his release, Windley expressed relief and happiness, noting that the ordeal had cost him nearly two decades of his life but he was grateful that justice was finally served.

Brooklyn District Attorney Eric Gonzalez also acknowledged that the conviction should never have occurred and expressed regret over Windley being wrongfully imprisoned.

The case highlights concerns over wrongful convictions and underscores the importance of thorough investigation and review in the justice system.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: