Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya na mataki mai kyau wajen cimma irin ci gaban da aka samu a ƙasashen Turai, musamman Ingila, idan aka yi la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da na zamantakewa.
A cikin jawabin da ya yi a wani taron ci gaban kasa, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa ta mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, inganta ayyukan more rayuwa, da samar da yanayi mai dorewa ga masu zuba jari. Ya ce, “Najeriya na tafiya kan hanyar da ta dace domin cimma matsayi kamar na Ingila a fannin ci gaba, musamman idan aka duba yadda muke bunkasa tattalin arzikinmu da kuma samar da damar rayuwa ga yan kasa.”
Shugaban ya kara da cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati da al’umma wajen ganin Najeriya ta cimma manyan manufofin ci gaba, ciki har da inganta ilimi, lafiya, da ayyukan sufuri. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai domin ganin kasar ta zama jagorar ci gaba a Afirka.
Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na da dukkan abubuwan da ake bukata, ciki har da dimbin matasa masu hazaka, albarkatun kasa, da tsarin mulki mai karfi, wanda zai bai wa kasar damar yin gogayya da manyan kasashen duniya wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Haka kuma, Shugaban ya nuna cewa Najeriya za ta ci gaba da neman sabbin hanyoyin inganta fasaha da kere-kere domin bunkasa masana’antu da samar da ayyukan yi ga al’umma.
Wannan jawabi na Tinubu ya fito ne a wani lokaci da kasar ke fuskantar kalubale na tattalin arziki da siyasa, inda yake ƙoƙarin tabbatar wa ‘yan kasa cewa Najeriya na kan hanya madaidaiciya ta ci gaba.
News Translation in English Language.
Nigeria Approaching UK-Level Development – President Tinubu.
President Bola Ahmed Tinubu has stated that Nigeria is making significant progress toward achieving a level of development comparable to that of the United Kingdom, citing ongoing economic and social reforms.
Speaking at a national development forum, President Tinubu said his administration is focused on strengthening the economy, improving infrastructure, and creating a conducive environment for investors.
“Nigeria is on the right path to attaining a level of development similar to that of the UK, especially considering the steps we are taking to grow our economy and improve the standard of living for our citizens,” he said.
The President emphasized the need for strong collaboration between the government and the public to achieve key development goals. These include improving education, healthcare, and transportation systems across the country. He also called on Nigerians to unite in efforts to position the nation as a leading force in Africa’s development.
Tinubu noted that Nigeria possesses vast potential, including a youthful and talented population, abundant natural resources, and a stable democratic system, all of which can enable the country to compete globally in economic and social development.
He further highlighted the government’s commitment to advancing technology and innovation as a means of boosting industrial growth and creating employment opportunities.
The President’s remarks come at a time when Nigeria is facing economic and political challenges, as his administration seeks to reassure citizens that the country is on a steady path toward sustainable development.

0 Comments:
Post a Comment