Jirgin farko ya sauka a Sabon filin jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Gusau Gabanin Ziyarar Manyan Baƙi.

Jirgin farko ya sauka a Sabon filin jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Gusau Gabanin Ziyarar Manyan Baƙi.

Jirgin farko ya sauka a Sabon filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa dake Gusau a wani muhimmin mataki na tarihi, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen karɓar manyan baƙi a jihar Zamfara.

Jirgin, ƙirar Bombardier Challenger 605 da gwamnatin tarayyar Najeriya ke sarrafawa, ya sauka da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi.

A cewar jami’an gwamnati, wannan saukar jirgin gwaji ne da aka gudanar domin tantance shirin filin jirgin kafin zuwan manyan jami’ai da ake sa ran za su ziyarci jihar nan ba da jimawa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da wannan gwaji ne bayan samun amincewa daga ma aikatar kula da zirga-zirgar Jiragen sama ta Najeriya (NCAA), wadda ta bayar da sahalewar domin saukar jirgin.

An kuma gudanar da aikin ne bisa ƙa’idar zirga-zirgar jirage ta gani da ido (Visual Flight Rules – VFR), wato a cikin lokacin rana, daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban tarihi, yana mai cewa jihar ta shafe sama da shekaru 30 ba tare da filin jirgin sama mai aiki ba.

Ana sa ran wannan ci gaba zai ƙara jawo hankalin masu zuba jari, da inganta hanyoyin sufuri, tare da buɗe ƙofofin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci a nan gaba.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: