Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Yi wa matasa aiki domin ladabtarwa.

Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Yi wa matasa aiki domin ladabtarwa.

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, reshen ƙaramar hukumar Sabuwa, ta yi wa wasu matasa masu ɗauke da askin banza aski domin ladabtarwa a yayin bukukuwan Sallah.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, 21 ga Maris, 2026, rundunar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne a wurare daban-daban na garin yayin bikin Sallah da ya gabata.

Shugaban Hisbah na Sabuwa, DC Malam Idris Hayatu, shi ne ya jagoranci wannan aikin.

Sanarwar ta ce: “Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, reshen Sabuwa, ta kaddamar da wani shiri na musamman mai taken Operation Happy Sallah a yau, Asabar, 21 ga Maris, 2026, domin tabbatar da zaman lafiya da tsafta yayin bukukuwan Sallah.”

“An gudanar da aikin ne a sassa daban-daban na garin Sabuwa, inda jami’an suka mayar da hankali wajen hana rashin hankali da dabi’u marasa kyau, da ayyukan kida da ke haddasa hayaniya da taruwar jama’a.”

Shugaban ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda, tare da kare mutuncin jama’a musamman a wannan lokaci mai muhimmanci.

Haka kuma, ya yi kira ga jama’a musamman matasa su rungumi kyawawan halaye, su guji duk wani hali da ka iya kawo rashin jituwa a cikin al’umma.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: