Jami'ar BUK Ta Kori Dalibai 171 Kan Jabun Takardun Shiga.

Jami'ar BUK Ta Kori Dalibai 171 Kan Jabun Takardun Shiga.

Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta kori dalibai 171 bayan an same su da laifin amfani da jabun takardun shaidar karatu domin samun gurbin karatu a jami’ar.

Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wani cikakken bincike da majalisar jami’ar ta gudanar kan sahihancin takardun shiga da daliban suka gabatar lokacin neman gurbin karatu.

A cewar jami’ar, an gano cewa wasu daga cikin daliban sun yi magudi wajen sauya maki a sakamakon jarabawarsu domin su dace da ka’idojin shiga jami’a. Haka kuma, wasu sun yi amfani da takardun wani mutum daban, yayin da wasu bayanansu suka yi sabani da na hukumomin jarrabawa kamar JAMB da WAEC.

Jami’ar ta ce wannan laifi ya saba da dokokinta, wanda ke tanadar da hukuncin kora kai tsaye ga duk wanda aka samu da irin wannan laifi.

A wani bangare kuma, an kori wani dalibi daban saboda cin zarafin masu sanya ido yayin gudanar da jarrabawa.

BUK ta jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya da ingancin ilimi, tana mai gargadin cewa za ta dauki mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu da aikata laifin karya dokokin jami’a.

News Translation in English Language.

Bayero University Kano Expels 171 Students Over Falsified Admission Credentials.

Bayero University Kano (BUK) has expelled 171 students after they were found to have used falsified academic credentials to secure admission into the institution.

The decision followed a comprehensive investigation conducted by the university’s Senate, which focused on verifying the authenticity of admission documents submitted by the affected students.

According to the findings, some of the students manipulated their examination scores to meet admission requirements, while others used impersonation by presenting documents belonging to different individuals. In several cases, discrepancies were discovered between the students’ records and official data from examination bodies such as the Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) and the West African Examinations Council (WAEC).

The university stated that such acts constitute a serious violation of its academic regulations, which prescribe expulsion as the appropriate sanction for admission fraud.

In a related development, the institution also expelled another student for assaulting examination invigilators during an exam.

BUK reaffirmed its commitment to maintaining academic integrity and standards, warning that it will continue to enforce strict disciplinary measures against anyone found guilty of violating its rules.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: