Isra’ila ta kashe Falasdinawa 5 a Sakamakon Hare-haren da taka kai zirin Gaza.

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 5 a Sakamakon Hare-haren da taka kai zirin Gaza.

Rundunar sojojin Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, inda aƙalla Falasdinawa biyar suka rasa rayukansu, a yayin da Hare-hare ya ƙaru a wannan yanki mai cike da tashin hankali. 
Rahotanni daga Gaza sun nuna cewa hare-haren sun yi sanadiyyar lalata gidaje da asibitoci, tare da jefa fararen hula cikin halin ƙunci.

Hare-haren sun zo ne a cikin wani lokaci da ake fuskantar ƙarancin abinci da magunguna da mafaka ga miliyoyin fararen hula a yankin.

A lokaci guda, rikicin ya watsu zuwa ƙasashen makwabta, inda Isra’ila ta kashe akalla ma’aikatan lafiya 12 a kudancin Lebanon, ciki har da likitoci da ma’aikatan jinya. Wannan ya nuna yadda rikicin ke ƙara girma zuwa wasu yankuna na yanki.

Tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma da Kungiyar Hamas da Israi'la a shekaran da ta gaba, hare-haren Israi'la akan Falasdinawa ba su tsaya ba, inda dubban fararen hula suka rasa rayukansu ko suka raunana, tare da jefa ma’aikatan lafiya da rayuwar yau da kullum cikin haɗari.

News Translation in English Language.

Israel Kills 5 Palestinians in Gaza Strikes.

The Israeli military continued air and ground strikes in the Gaza Strip, killing at least five Palestinians as tensions escalate in the conflict-ridden territory.

Reports from Gaza indicate that the attacks have caused widespread destruction of homes and hospitals, leaving civilians in dire conditions. The strikes come amid a severe shortage of food, medicine, and shelter for millions of residents.

Meanwhile, the conflict has spread to neighboring countries, with Israel reportedly killing at least 12 healthcare workers in southern Lebanon, including doctors and nurses, highlighting the regional escalation of violence.

Since the ceasefire agreement between Hamas and Israel last year, Israeli attacks on Palestinians have persisted, resulting in thousands of civilian deaths and injuries, and putting healthcare workers and everyday life at significant risk.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: