Ƙasar Iran ta ce babu wanda zai Hana tawagar Ƙwallon Kafar ƙasar Halartar Gasar Kofin Duniya, duk da Gargadin Donald Trump.

Ƙasar Iran ta ce babu wanda zai Hana tawagar Ƙwallon Kafar ƙasar Halartar Gasar Kofin Duniya, duk da Gargadin Donald Trump.

Ƙasar Iran ta bayyana cewa ba wanda zai iya hana ta shiga gasar cin Kofin Duniya da za a gudanar a wannan shekaran, bayan gargadin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa “rayuwa da tsaron” ‘yan wasanta na iya fuskantar haɗari idan suka je Amurka.

A cikin wani sako da tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Alhamis, ta jaddada cewa dole ne a ba dukkan ƙasashe damar shiga gasar ba tare da tsangwama ba, tare da cewa ba za a iya ware Iran daga irin wannan babbar gasa ta duniya ba.

Tawagar ta kuma bayyana cewa bai kamata Amurka ta kasance cikin ƙasashen da za su karɓi bakuncin gasar ba, idan har ba za ta iya tabbatar da cikakken tsaron dukkan ƙungiyoyin da za su halarta ba.

Kalaman Trump sun zo ne kwana biyu bayan da ya gaya wa shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Gianni Infantino, cewa  za'a yi maraba da 'yan wasan a Amurka, duk da rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa wannan muhawara ta sake jawo hankali kan batun siyasa da tsaro a gasannin wasannin na duniya, musamman yayin da ake shirin gudanar da FIFA World Cup a Amurka tare da haɗin gwiwar Kasashen Amurka da Kanada da Mexico.

News Translation in English Language.

Iran Says No One Can Bar Its Team From the World Cup Despite Trump Warning.

Iran has declared that no one can prevent its national football team from participating in the upcoming World Cup, despite a warning from US President Donald Trump that the “life and safety” of Iranian players could be at risk if they travel to the United States.

In a statement posted on social media on Thursday, Iran’s national team stressed that all countries must be allowed to take part in the tournament without discrimination, adding that Iran cannot be excluded from such a major global competition.

The team also argued that the United States should not be among the host countries if it cannot guarantee the safety and security of all participating teams.

Trump’s remarks came two days after he told FIFA President Gianni Infantino that Iranian players would be welcomed in the United States, despite the ongoing tensions and conflict in the Middle East.

Reports indicate that the dispute has once again drawn attention to the role of politics and security in international sports, particularly as preparations continue for the FIFA World Cup, which will be co-hosted by the United States, Canada, and Mexico.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: