Iran Ta Kama Mutane 500 Kan Zargin Leƙen Asiri Ga Maƙiyanta.

Iran Ta Kama Mutane 500 Kan Zargin Leƙen Asiri Ga Maƙiyanta.

Jami’an tsaron Iran sun bayyana cewa sun kama mutane kusan 500 da ake zargi da yin leƙen asiri ga maƙiyan ƙasar, a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran da hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ke ƙaruwa.

Babban shugaban ‘yan sandan ƙasar, Janar Ahmadreza Radan, ya ce mutanen da aka kama suna da hannu a ba da bayanai kan wuraren da aka kai hare-hare da ɗaukar bidiyo ko hotuna na wuraren da aka kai harin da tura bayanai ga maƙiya.

Jami’an sun bayyana cewa kimanin rabin waɗanda aka kama suna da hannu a manyan laifuka, yayin da wasu ke aiki a wata ƙungiyar leƙen asiri da aka tarwatsa a wasu larduna uku na ƙasar.

Haka kuma, wasu daga cikin waɗanda aka kama suna tura bayanai ga tashar talabijin ta waje, mai suna 'Iran International', wadda gwamnatin Iran ta ɗauka a matsayin ƙungiya mai adawa da ita.

Hukumar tsaro ta ce wannan mataki na zuwa ne ne sakamakon matsin lamba daga hare‑haren da ake kaiwa a ƙasar, lamarin da ya sa aka tsaurara matakan tsaro a fadin Iran.

News Translation in English Language.

Iran Arrests 500 Suspected Spies Amid Rising Tensions with US and Israel.

Iranian security forces have announced the arrest of approximately 500 individuals suspected of spying for the country’s enemies, amid escalating tensions between Iran and the US-Israel alliance.

Chief of Police, General Ahmadreza Radan, stated that the suspects were involved in providing intelligence on attack sites, taking photos or videos of targeted locations, and transmitting information to hostile actors.

Authorities said about half of those arrested were linked to major crimes, while others were part of a dismantled espionage network operating in three Iranian provinces.

Some of the detainees were also accused of sending information to the foreign-based television channel “Iran International,” which the Iranian government considers an opposition outlet.

The security agency emphasized that the crackdown comes in response to ongoing attacks within the country, prompting heightened security measures across Iran.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: