An Ji Ƙarar Fashe-Fashe a birnin Tel Aviv na Israi'la Bayan Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami.

An Ji Ƙarar Fashe-Fashe a birnin Tel Aviv na Israi'la Bayan Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami.

Da sanyin safiyar yau Litinin, an ji ƙarar ƙararrawar gaggawa ta tsaro a sassa daban-daban na birnin Tel Aviv da ke cikin Israi'la, lamarin da ya sa mazauna garin suka garzaya zuwa wuraren kariya.

Rahotanni sun ce jim kaɗan bayan ƙararrawar ta tashi, an ji jerin ƙarar fashe-fashe a wasu sassan birnin. Wannan na zuwa ne bayan dakarun juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, IRGC sun bayyana cewa sun harba wasu makamai masu linzami zuwa Isra’ila a wani sabon mataki na hare-haren ramuwar gayya.

A cewar rahotannin baya-bayan nan, hare-haren makamai masu linzami daga Iran sun rika haddasa ƙararrawar tsaro a birane da dama na Isra’ila, inda jami’an tsaron ƙasar ke ƙoƙarin kakkabe makaman ta hanyar tsarin kariya na sama. 

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani kan irin ɓarnar da aka samu ko asarar rayuka ba, yayin da hukumomin tsaron Isra’ila ke ci gaba da bibiyar lamarin.

Wannan sabon farmaki na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ke ƙara tsananta, inda ɓangarorin biyu ke musayar hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya. 

News Translation in English Language.

Explosion Sounds Reported in Tel Aviv After Iran Launches Missiles at Israel.

Early Monday morning, security alarms were triggered across various parts of Tel Aviv, Israel, prompting residents to seek shelter. Shortly after the alerts, a series of explosions were reported in several areas of the city.

The Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) of Iran claimed responsibility for launching missiles toward Israel in what appears to be a retaliatory strike. Reports indicate that the missile attacks have activated Israel’s air defense systems, with authorities working to intercept the incoming projectiles. (wsj.com)

As of this report, there is no confirmed information on casualties or the extent of property damage, while Israeli security forces continue to monitor the situation closely.

The latest missile strikes come amid escalating tensions between Iran and Israel, with both sides exchanging attacks in the Middle East region. (theguardian.com)


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: