Gwamna Dauda Lawal na cikin Tawagar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Ziyarar Aiki zuwa Birtaniya.

Gwamna Dauda Lawal na cikin Tawagar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Ziyarar Aiki zuwa Birtaniya.

Gwamna Dauda Lawal na cikin manyan jami’an gwamnati da ke tare da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a tawagar da za ta kai ziyarar aiki zuwa ƙasar Birtaniya.

Shugaban ƙasa da uwargidansa za su tashi daga Abuja yau Talata domin fara wannan ziyarar mai muhimmanci, wadda ake sa ran za ta tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi dangantakar diplomasiyya da kasuwanci da tsaro tsakanin Najeriya da Kasar Birtaniya.

Haka kuma, an bayyana cewa Gwamna Lawal zai samu damar yin ganawa da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabannin kasuwanci a London domin bunkasa jarin waje da shigar sabbin hanyoyin ci gaba ga jiharsa da ƙasa baki ɗaya.

Tawagar za ta kasance cikin wani tsari na taron aiki, hadakar tattaunawa da ziyartar wasu cibiyoyi na gwamnati da na kasuwanci, inda ake sa ran samar da sabbin yarjejeniyoyi da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Hukumomin Najeriya sun ce ziyarar za ta kara karfafa dangantaka mai dorewa tsakanin ƙasashen biyu, tare da bai wa gwamnoni da manyan jami’ai damar yin hulɗa kai tsaye da masu ruwa da tsaki a harkokin diflomasiyya da tattalin arziki.

News Translation in English Language.

Governor Dauda Lawal Joins President Bola Ahmed Tinubu’s Official Visit to the United Kingdom.

Governor Dauda Lawal is among the senior government officials accompanying President Bola Ahmed Tinubu on an official working visit to the United Kingdom.

The President and his wife are scheduled to depart from Abuja on Tuesday to begin the important visit, which is expected to focus on diplomatic, trade, and security relations between Nigeria and the United Kingdom.

Governor Lawal is also set to meet with senior government officials and business leaders in London to promote foreign investment and explore new development opportunities for his state and the country as a whole.

The delegation’s schedule includes official meetings, discussions, and visits to government and business institutions, where new agreements and partnerships between the two countries are expected to be established.

Nigerian authorities stated that the visit will strengthen long-term relations between Nigeria and the UK and provide governors and senior officials with the opportunity to engage directly with key stakeholders in diplomacy and economic development.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: