Iyalai na ci gaba Neman ‘Yan Uwansu Bayan harin da Pakistan ta kai kan cibiyar jinyar masu shan miyagun kwayoyi a birnin Kabul na ƙasar Afghanistan.
Mahukuntan ƙasar Afghanistan sun bayyana cewa harin ya kashe mutane kusan 408, bayan da aka kai shi kan asibitin "Omar Addiction Treatment" da misalin ƙarfe 9 na dare agogon ƙasar.
Wani mazaunin yankin, Baryalai Amiri mai shekaru 38, ya je cibiyar domin neman ɗan’uwansa da aka kwantar a asibitin kusan kwanaki 25 da suka gabata.
Ya ce har yanzu babu cikakken bayani daga jami’ai kan halin da ake ciki.
“Ba a ba mu cikakken bayani ba. Har yanzu ba mu san inda yake ba,” in ji shi, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da tono baraguzan ginin da ya rushe.
Rahotanni sun nuna cewa dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta yi tsami cikin watanni da suka gabata, inda Pakistan ke zargin Afghanistan da bai wa kungiyoyin ‘yan bindiga mafaka, wadanda ke kai hare-hare a kan iyakan Kasashen.
Sai dai gwamnatin Pakistan ta musanta zargin kai wannan hari, tana mai cewa ikirarin da aka yi ba gaskiya ba ne.
News Translation in English Language.
Families Continue Search for Loved Ones After Alleged Pakistan Strike on Afghan Rehab Centre.
Families are continuing to search for their missing relatives following an alleged airstrike by Pakistan on a drug rehabilitation centre in Kabul, the capital of Afghanistan.
Afghan authorities said the attack killed about 408 people after it struck the “Omar Addiction Treatment” hospital at around 9:00 pm local time.
A resident, 38-year-old Baryalai Amiri, visited the facility in search of his brother, who had been admitted to the centre about 25 days earlier. He said there has been no clear information from officials regarding the situation.
> “We have not been given proper information. So far, we do not know where he is,” he said, as rescue workers continued to search through the rubble of the destroyed building.
Reports indicate that tensions between Afghanistan and Pakistan have escalated in recent months, with Islamabad accusing Kabul of harboring armed groups responsible for cross-border attacks.
However, the Pakistani government has denied carrying out the strike, describing the claims as false.

0 Comments:
Post a Comment