Aƙalla masu ibada tara ne ake zargin ’yan bindiga sun sace da sanyin safiyar Lahadi a Cocin St. John’s Catholic Church da ke Ojije, a gundumar Utonkon, Ƙaramar Hukumar Ado ta Jihar Benue.
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa ’yan jarida a yau Litinin cewa ’yan bindigar sun mamaye cocin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, yayin da masu ibadar ke tsaka da gudanar da addu’ar dare (night vigil).
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Ci gaban Ufia a Ƙaramar Hukumar Ado, Jude Onwe, ya ce waɗanda aka sace sun haɗa da mata da matasa, adadinsu ya kai kusan tara.
“Da misalin ƙarfe 2 na dare ranar Lahadi, waɗannan mata da matasa—kimanin masu ibada tara—aka sace su daga Cocin St. John’s Catholic Church da ke Ojije a Utonkon, Ƙaramar Hukumar Ado, yayin da suke gudanar da addu’ar dare,” in ji shi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ado, Sunday Oche, ya kuma tabbatar da lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa sace-sacen ya faru ne yayin wani shirin addu’a na dare da ake gudanarwa a matsayin wani ɓangare na shirin ibada na kwanaki 30.
Oche ya nuna takaicinsa kan yadda masu shirya shirin suka yi watsi da shawarwarin da aka ba su na haɗa jami’an tsaro a irin waɗannan ayyuka na dare.
Ya ce tuni ƙaramar hukumar ta sha faɗakar da al’umma cewa duk wani taro ko shiri da zai wuce ƙarfe 9 na dare ya kamata a sanar da jami’an tsaro.
“Mun samu wannan mummunan labari na sace mutanen, kuma na riga na tura dukkan hukumomin tsaro.
Ana aiki tukuru domin ganin an ceto su,” in ji Oche. “Mun riga mun yi gargaɗi cewa duk wanda zai shirya wani shiri, musamman da daddare, dole ne ya haɗa jami’an tsaro.
Idan aka yi shiri na tsawon kwanaki ba tare da sanar da hukumomin tsaro ba, to an jefa rayukan mutane cikin haɗari.”
Ya kuma tuna wani lamari makamanci a baya inda aka yi yunƙurin sace mutane, amma jami’an tsaro suka yi gaggawar kai ɗauki tare da ceto waɗanda abin ya shafa.
Ya tabbatar da cewa ana bin sahun ’yan bindigar, tare da ba da tabbacin cewa za a ceto masu ibadar da aka sace.
“Muna tabbatar wa da jama’a cewa za a ceto waɗanda aka sace. Jami’an tsaro suna kan bin sawun ’yan bindigar, kuma a halin yanzu al’amura sun daidaita a yankin,” in ji shi, yana mai ƙara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin tsaro a yankin.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue ta tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya ce an tura tawagar musamman ta jami’an tsaro zuwa yankin domin aikin ceto.
“Tuni an tura tawagar musamman domin ceto waɗanda aka sace,” in ji Edet.
Wannan sabon lamari na sace-sace ya sake jaddada ƙalubalen tsaro da ke ƙara ƙamari a Jihar Benue, musamman bayan kisan gillar da ya faru a yankin Yelwata a watan Yuni na bara, inda kusan mutane 200 suka rasa rayukansu—lamarin da ya jawo tirjiya da Allah-wadai daga ciki da wajen ƙasar nan.
%20(1)_1.webp)
0 Comments:
Post a Comment