Mazauna unguwar Danhonu II da ke New Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin, sakamakon yawaitar sace-sacen mutane, biyo bayan sace mutane bakwai da ake zargin ‘yan bindiga ne suka aikata.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Millennium City Division, inda suka tare babbar hanya, suna rera wakokin nuna hadin kai tare da bukatar daukar matakin gaggawa na tsaro.
Rahotanni sun ce sabon harin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare ranar Lahadi, inda wasu dauke da makamai suka mamaye unguwar suka sace mambobin iyalai biyu.
An bayyana sunayen wadanda aka sace da suka hada da Malam Yahaya Yusuf da matarsa Latifat, da ‘ya’yansu Abdulgafar da Abdulqudus.
Haka kuma an sace Mrs Abdulrazak Jimoh tare da ‘ya’yanta biyu, wadanda har yanzu ba a bayyana sunayensu ba.
Mazauna unguwar sun ce lamarin ya kara jefa tsoro a zukatansu, tare da bayyana cewa yanzu adadin sace-sacen da aka samu a yankin ya kai 11 cikin ‘yan watanni kadan.
Sun yi zargin cewa galibin hare-haren na mayar da hankali ne kan wadanda ba ‘yan asalin yankin ba, lamarin da ya haifar da zargin cewa wasu masu ba da bayanai na taimaka wa ‘yan bindigar.
Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun shigo unguwar da yawa kuma dauke da muggan makamai.
“Cikin watan da ya gabata kadai, fiye da mutane hudu aka sace a nan. Jiya kuma, ‘yan bindiga kusan su 15 dauke da bindigogin AK-47 suka shigo suka sace akalla mutane bakwai zuwa wani wuri da ba a sani ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa mazauna unguwar sun yanke shawarar zuwa ofishin ‘yan sanda ne domin gabatar da koken su bayan jurewa hare-hare da dama da suka yi a baya.
Shugaban Kungiyar Masu Gidaje ta Danhonu II kuma jagoran zanga-zangar, Malam Akoh Salifu, ya ce al’ummar unguwar ba sa iya rayuwa cikin kwanciyar hankali sakamakon yawaitar sace-sace.
“Muna nan ne domin ba za mu iya ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya ba. Matsin lambar wadannan hare-haren sace-sace ya yi yawa matuka,” in ji Salifu.
Ya bayyana cewa wasu matasa sun yi yunkurin bin ‘yan bindigar zuwa cikin daji bayan harin daren Lahadi, amma ba su samu nasarar kama su ba.
“A matsayarmu na ‘yan kasa masu bin doka, mun yanke shawarar zuwa wurin ‘yan sanda domin gabatar da kokenmu tare da neman daukin gaggawa don ceton al’ummarmu,” Inji Shi.
Da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta samu kiran gaggawa kuma ta dauki matakin kai dauki.
Hassan ya ce ‘yan sanda tare da sojoji sun isa wurin, amma sun makara sakamakon mummunan yanayin hanya da wahalar shiga yankin, lamarin da ya bai wa ‘yan bindigar damar tserewa duk da musayar wuta.
Ya kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya ziyarci unguwar inda ya gana da masu ruwa da tsaki, tare da ba su tabbacin cewa rundunar za ta yi la’akari da kafa ofishin ‘yan sanda (outpost) a yankin.
Tags
Labarai
