Gurfanar da Limamin masallaci, Imam Abdulgafar Sakariyah, mai shekaru 51, tare da wasu mutum huɗu, bisa zargin kisan kai, ya sake jawo hankalin jama’a kan hatsarin hukuncin taron dangi (mob justice) a Jihar Osun, tare da ƙarin kira ga gwamnati da ta girka kyamarorin sa ido (CCTV) a wuraren jama’a.
An gurfanar da Sakariyah da sauran waɗanda ake tuhuma a Kotun Majistare ta Osogbo, inda aka tsare su kan mutuwar Ahmed Najeem, wanda aka ce taron jama’a sun doke shi bayan da ake zargin ya yi yunƙurin kai wa limamin hari a lokacin sallar asuba a Masallacin Ummu Haani Adigun Memorial Central a ranar 30 ga Janairu.
Baya ga tuhumar kisan kai, lamarin ya sake tayar da damuwa kan yawaitar hukuncin taron dangi a jihar, wanda masu suka ke cewa sau da yawa yana barin ainihin masu laifi su tsere, yayin da wasu da ba su aikata laifi kai tsaye ba ke fuskantar shari’a.
Yadda lamarin ya faru
Shaidu sun ce a safiyar Juma’ar ranar, yayin da Imam Sakariyah ke gabatar da wa’azi bayan sallar asuba, wani mai ibada mai suna Ahmed Najeem ya taso ya ƙwace sandar makirufo, ya nufi limamin da ita. Limamin ya kauce wa harin, ya tsere. Daga nan ne aka ce wasu masu ibada suka kama Najeem, suka ja shi waje, inda aka yi masa duka da sanduna da bugun jiki, aka bar shi a cikin magudanar ruwa yana zubar da jini a kai da wuya.
Wasu shaidu sun ce duk da raunukan da ya samu, Najeem yana raye lokacin da ‘yan sanda suka iso suka ɗauke shi. Daga bisani aka ce ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti sakamakon munanan raunukan da aka yi masa.
Bayanin ‘yan sanda
Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da cewa ba a kashe Najeem a cikin masallaci ba, sai dai “a kusa da harabar masallacin.” Ya ce bincike na gudana domin gano duk masu hannu a lamarin, yayin da aka ajiye gawar mamacin a dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jihar Osun.
Tashin hankali da kama mutane
Bayan yaɗuwar labarin mutuwar Najeem, an samu tashin hankali a yankin. ‘Yan uwan mamacin sun yi zanga-zanga a masallacin, suna barazanar ƙone ginin kafin sallar Juma’a. Don hana rikici, ‘yan sanda daga Sashen Ataoja suka koma wurin, suka kwashe limamin da wasu masu ibada huɗu.
A gaban Majistare A. Daramola, kotu ta amince da bukatar tsare waɗanda ake tuhuma a Gidan Gyaran Hali na Ilesa domin jiran shawarwarin shari’a daga Ofishin Daraktan Gurfanar da Kara (DPP). An dage sauraron shari’ar zuwa 24 ga Fabrairu, 2026.
Kiran adalci
‘Yan uwan mamacin sun musanta ikirarin cewa Najeem na fama da matsalar tabin hankali, suna neman a cafke tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi. Wasu shaidu kuma sun ce da yawa daga cikin waɗanda suka doke Najeem sun tsere, suna zargin cewa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ba su shiga dukan kai tsaye ba.
Allah-wadai da kiran girka kyamarori
Tsohon Darakta-Janar na Osun Amotekun, Amitolu Shittu, da jagoran farar hula Wole Oladapo, sun yi Allah-wadai da kisan, suna kira ga ‘yan sanda da su tabbatar da cewa ainihin masu laifi ba su tsere ba. Sun kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta gaggauta girka kyamarorin CCTV a fadin jihar domin hana aikata laifuka da sauƙaƙa gano masu aikata su.
Shittu ya ce, “Hukuncin taron dangi abin ƙyama ne kuma dole a kawo ƙarshensa. Duk wanda ya aikata laifi ya fuskanci hukuncin doka.” Oladapo ya ƙara da cewa, “Idan aka girka kyamarori a ko’ina, babu wanda zai tsere daga adalci.”
Tags
Labarai
