Harin da Isra’ila ta kai kan wani gini a Gaza ya kashe Falasɗinawa huɗu.

Harin da Isra’ila ta kai kan wani gini a Gaza ya kashe Falasɗinawa huɗu.

Aƙalla Falasɗinawa huɗu ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan sojojin Isra’ila sun kai harin bama-bamai kan wani gini da ke ba wa ‘yan gudun hijira mafaka a birnin Gaza. 
Harin ya sake zama keta yarjejeniyar “tsagaita bude wuta” na watan Oktoba.

Harin saman ya auku ne a unguwar Nassr dake zirin Gaza, lamarin da ya ƙara yawan mutanen da aka kashe a ranar Litinin zuwa aƙalla bakwai.

Bidiyoyin da suka fito daga wurin sun nuna jami’an agaji na kwashe waɗanda suka jikkata cikin motocin asibiti, yayin da mazauna yankin ke ɗauke da gawar wani mutum zuwa sashen ajiye gawa na Asibitin Al-Shifa.

Wakilin kafar talabijin na Al Jazeera ya bayar da rahoton cewa, ginin da aka kai wa harin ya riga ya lalace sakamakon yaƙin Isra’ila a Gaza, kuma ana amfani da shi a matsayin mafaka ga Falasɗinawa ‘yan gudun hijira.

“An tilasta wa mutane neman mafaka a wannan ginin da ya riga ya lalace sakamakon ƙarancin matsuguni, bayan rusa yawancin gidajen zama a Gaza,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Wannan hari ya jefa jama’a cikin fargaba tare da barin su cikin damuwa kan abin da ka iya biyo baya, duba da wannan sabon tashin hankali da sojojin Isra’ila suka haifar.”

A cewar hukumomin Gaza, Isra’ila ta keta yarjejeniyar “tsagaita bude wuta” da Amurka ta shiga tsakani wajen kullawa har sau 1,520 tun bayan fara aikinta a ranar 10 ga Oktoban 2025. 
Tun daga lokacin, aƙalla mutane 581 ne suka mutu, yayin da 1,553 suka jikkata.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form