Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, kan zargin rashin da’a, tana mai cewa Majalisar ta yi hakan ne bisa ikon da doka ta tanada mata.
A hukuncin bai ɗaya da alkalai uku suka yanke hukuncin, kotun ta ce ta gamsu cewa dakatarwar ba ta tauye ’yancin majalisa ko ’yancin kundin tsarin mulki na Sanatar ba.
Sai dai kuma, kotun ta soke shari’ar cin mutunci da kuma tarar Naira miliyan biyar (₦5m) da aka kakaba mata, waɗanda suka samo asali daga neman yafiya ta barkwanci da ta gabatar wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Haka kuma, a hukuncin da Mai Shari’a A. B. Muhammed ya karanta, kotun ta ce Shugaban Majalisar Dattawa bai yi kuskure ba da ya hana Sanatar damar yin magana a zaman majalisa na ranar 20 ga Fabrairu, 2025, domin ba ta zauna a kujerar da aka ware mata a hukumance ba.
Kotun ta bayyana cewa, bisa ƙa’idojin Majalisar Dattawa, Shugaban Majalisa na da ikon ware kujeru ga ’yan majalisa, kuma doka ta tanadi cewa ’yan majalisa su yi magana ne kawai daga kujerun da aka ware musu.
Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida, wanda dakatarwar ta fara aiki daga 6 ga Maris, 2025, kan zargin rashin da’a da kuma karya ƙa’idojin Majalisar Dattawa na 2023 (da aka yi wa gyara).
An ɗauki matakin dakatarwar ne bayan rigimar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan batun tsarin zama a zauren majalisa.
_5.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment