An yaba wa wani jami’in ‘yan sanda a Jihar Borno, mai suna Mohammad Muhammad, bisa nuna gaskiya da rikon amana bayan da ya mayar da naira miliyan ₦2.6 da aka tura masa ta banki bisa kuskure daga wani kwastoman kamfanin moniepoint.
Yabon ya biyo bayan wani rubutu ne da wani mai suna Bello Jafar ya wallafa a shafin Facebook a ranar Juma’a, inda ya jinjina wa jami’in bisa abin da ya kira kyakkyawan misalin gaskiya da nagarta da ba kasafai ake samu ba.
A cewar Jafar, Mohammad Muhammad, jami’in ‘yan sanda kuma kwastoman United Bank for Africa (UBA), An tura mashi kudin ne bisa kuskure daga wani kwastoman Moniepoint, amma bai yi shiru ko anfani da kudin ba. Maimakon haka, ya dauki matakai domin gano asalin kudin tare da tabbatar da an mayar da su ga wanda suka dace.
“Ina so in bayyana godiya ta ga Mohammad Alhaji Muhammad, kwastoman UBA kuma jami’in ‘yan sanda mai cikakken gaskiya,” in ji Jafar.
“Bayan karɓar kudin bisa kuskure, ya yi duk mai yiwuwa domin gano bankin da aka tura kudin daga gare shi tare da tabbatar da an mayar da su gaba ɗaya ga mai su.”
Jafar ya bayyana wannan aiki a matsayin nuna kyawawan dabi’u, rikon amana da ladabi na aiki.
Ya ce, “Wannan abu ya nuna gaskiya, alhakin aiki da tsayin daka na ɗabi’a, kuma ya dace da abin da ake tsammani daga jami’in ‘yan sanda.”
Ya kara da cewa irin wannan aiki na taimakawa wajen inganta yadda jama’a ke kallon jami’an tsaro, tare da karfafa amincewa tsakanin al’umma da hukumomi.
A gefe guda, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da lamarin, inda kakakin rundunar, Nahum Daso, ya wallafa shaidar karɓar kudin da mayarwa da ke nuna an dawo da ₦2,618,720 a ranar Litinin. An wallafa shaidar tare da taken: “AN YABA WA JAMI’IN ‘YAN SANDA DA YA MAYAR DA MILIYAN ₦2.6 DAGA TURA KUDI BISA KUSKURE.”
Wannan yabo ya zo ne a daidai lokacin da rundunar ke ci gaba da shirye-shiryen horaswa da nufin inganta kwarewa da ladabi da mutunta hakkin dan Adam a tsakanin jami’ai a Maiduguri da sauran sassan jihar.

0 Comments:
Post a Comment