Dan bindigan da ya kashe Musulmai 51 a masallatai biyu a ƙasar New Zealand a shekarar 2019, ya nemi a sake yi masa sabuwar shari’a.

Dan bindigan da ya kashe Musulmai 51 a masallatai biyu a ƙasar New Zealand a shekarar 2019, ya nemi a sake yi masa sabuwar shari’a.

Brenton Tarrant, ɗan bindiga kuma mai ra’ayin wariyar launin fata da ya kashe Musulmi 51 a masallatai biyu a birnin Christchurch na ƙasar New Zealand a shekarar 2019, ya nemi a sake yi masa shari’a, yana mai cewa ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya amsa laifukan da aka tuhume shi da su.

Tarrant, mai shekaru 35 kuma ɗan ƙasar Australia, ya bayyana a gaban kotu a birnin Wellington ta hanyar bidiyo a yau Litinin, inda ya bayar da shaida a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara. 
Ya ce tsauraran yanayin da aka tsare shi a gidan yari sun lalata lafiyar kwakwalwarsa, wanda hakan ya sa bai cancanci yanke shawara mai ma’ana ba a lokacin da ya amsa laifi.

A watan Maris na 2019, Tarrant ya buɗe wuta a masallatan Al Noor da Linwood yayin sallar Juma’a, inda ya kashe mutane 51 tare da jikkata wasu da dama. 
Harin ya zama mafi muni wajen kisan gilla ta hanyar harbin bindiga a tarihin New Zealand. Ya kuma yi amfani da bindigogi irin na soja tare da watsa harin kai tsaye a shafin Facebook.

Da farko ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, yana shirin fuskantar shari’a, amma daga bisani ya amsa laifuka 51 na kisan kai, tuhume-tuhume 40 na yunkurin kisan kai da kuma laifi guda na aikata ta’addanci.

A cewar bayanan kotu, Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta bincika ko Tarrant bai da ikon yanke shawara mai ma’ana a lokacin da ya amsa laifukan, sakamakon yanayin tsarewa da ya bayyana a matsayin mai tsanani da rashin jin ƙai.

A halin yanzu, Tarrant na zaman gidan yari na har abada ba tare da damar neman afuwa ba, hukuncin da ya zama na farko irinsa a tarihin shari’ar New Zealand.

An shirya sauraron ƙarar na tsawon kwanaki biyar, kuma ana sa ran kammala shi a ranar Juma’a. 
Idan kotu ta ki amincewa da bukatar soke amincewarsa da laifukan, za a sake sauraron ƙarar hukuncinsa daga baya a shekarar. 
Idan kuma aka soke tuhumar, za a mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun ƙasar domin a sake yi masa shari’a.

Iyalan wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu sun hallara a kotun Wellington domin sauraron shaidarsa. 
Rashid Omar, wanda ɗansa Tariq ya rasu a harin, ya bayyana cewa matakin na Tarrant “ɓata lokaci ne da kuɗin masu biyan haraji,” yana zargin sa da ƙoƙarin ƙara jefa iyalan cikin raɗaɗi.

Bayan harin na 2019, gwamnatin New Zealand ta tsaurara dokokin bindiga domin hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a ƙasar.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: