Rushewar Gine-gine a Arewacin Lebanon ya Kashe Mutane 9
A kalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da gine-gine biyu da ke makwabtaka da juna suka rushe a birnin Tripoli, a arewacin Lebanon, kamar yadda jami’an gwamnati ƙasar suka sanar.
Shugaban hukumar kariyar fararen hula, Imad Khreish, ya bayyana wa manema labarai cewa mutum tara ne suka mutu, yayin da wasu shida da aka ceto aka kai su asibiti. Gine-ginen sun kunshi gida biyu, kowanne na dauke da dakuna shida, kuma mazauna wajen sun kiyasta cewa mutane 22 ne suke cikin gine-ginen a lokacin da rushewar ta faru.
Ayyukan ceto suna ci gaba, inda jami’an kariyar farar hula tare da Red Cross na Lebanon da sauran hukumomin ayyukan jin kai ke jagorantar.
Mazauna unguwar ma suna taimakawa wajen cire tarkace da bude hanyoyi a cikin gine-ginen da suka rushe.
Wani dattijo a Tripoli, Abdel Hamid Karimeh, ya bayyana cewa: “Muna ayyana Tripoli a matsayin birni mai tsarin gaske saboda gine-gine marasa tsaron lafiya.
Dubban mutanenmu na cikin hadari sakamakon shekaru da aka yi ana watsi da su. Lamarin ya wuce iyawar hukumar birnin Tripoli.”
Hukumomin tsaro da ‘yan sandan Tripoli sun kwashe mazauna daga gidaje masu makwabtaka da inda ginin ya rushewar saboda tsoron lafiyarsu, a cewar hukumar labarai ta ƙasar Lebanon (NNA).
Shugaban ƙasar, Joseph Aoun ya umarci dukkan hukumomin gaggawa su kasance cikin shiri don taimakawa ayyukan ceto da bayar da mafaka ga mazauna gidajen da ke kusa.
Shima Firaminista Nawaf Salam ya tabbatar da cewa gwamnati ta shirya bayar da tallafin mazaunin gidaje ga duk wanda ake bukatar kwashe shi daga gidajen da suke da hadarin zama.

0 Comments:
Post a Comment