Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata tawaga daga ƙasar Amurka ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka (USAFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Tawagar ta haɗa da Mukaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Mista Keith Heffern, tare da wasu manyan jami’an rundunar sojin Amurka.
Taron ya gudana ne a State House, inda Shugaba Tinubu ya tarbi baƙin, tare da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, da kuma shugabannin rundunonin tsaron ƙasar nan.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Sadarwa, Mista Dada Olusegun, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da Mai Ba Shi Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da shugabannin rundunonin tsaro, sun karɓi Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka, Janar Dagvin Anderson, tawagarsa, da Mukaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Keith Heffern, a fadar gwamnati dake Abuja.”
Duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanan tattaunawar da aka yi a bayan fage ba, ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Haka kuma, wannan ganawa na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa Amurka ta tura ƙaramin rukuni na sojojinta zuwa Najeriya a ranar 3 ga Fabrairu, lamarin da ya zama farkon shigar sojojin Amurka ƙasar nan a hukumance tun bayan hare-haren sama da aka kai kan sansanonin ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto da kwara a ranar Kirsimeti ta shekarar 2025.

0 Comments:
Post a Comment